Lyrics

Soyayya ta hada mu dake yan mata
Soyayya ta hada mu da kai dan gata
Kar ki manta
Alkawar' ki rike
Kinji masoyiya
Zuciya ta in babu ke ta sude
Zan kasa moriya
Zantukan ki
Su kadai na tuna
Suna sani dariya
Kina fadi zaki rayu dani
In nayi cuta kece magani
Soyayya ta rike mu
Har zuwa wannan lokaci, wannan lokaci
Kyakkyawa kai ne a sahun farko
Ina da tabbaci, ina da tabbaci
Zan zamto mai kara ma matsaya
A kowane lokaci
Kowane lokaci
Da kai kira ba jira na taho
Ni sai da kai zan cike burin rai na
Kina da kyau
Tamkar Naira gun mai nema, mai nema
Bani babu yawo
Idan kinka zamo a dama, a dama
In har mun kasance da juna
Bama yin nadama-nadama
Karatu ke kike gyara min
In na bace sai ki tayar dani
Na fito ran Litinin
Kai kuma Juma'a ranar ka fito
Mun a ran gama sa'ilin da zuciyoyin mu
Suke ambato
Ka amince na amince
Tsakaninmu ka fito na fito
Da safe kafin a wayi gari
In saka baci domin haka ne kauna
Soyayya ta hada mu dake yan mata
Soyayya ta hada mu da kai dan gata
Written by: Abdul D One
instagramSharePathic_arrow_out