Top Songs By Umar M Shareef
Lyrics
Maya
Nice Maya
Maya ke nake wa soyayyata
Zuciya dake kadai tai yarda
Maya kai nake wa soyayyata
Zuciya dakai kadai tai yarda
Nice Maya
In akwai rikon amana yafi
Lafiya qalau a zauna ba zafi
Inda yarda zama zaiyo zurfi
Sirrika na juna a rufe asa murfi
Mai zuwa da gulma a kifa mar tafi
Tunda shi yake raba so da kauna
Maya kai nake wa soyayyata
Zuciya dakai kadai tai yarda
Lafiyarki lafiyata ce
Damuwarki damuwata ce
Duk abinda nai kawai kece
Karku tuntube ni kauna ce
So in yayai zurfi a rai ila ne
Tunda ana rasa rai kan kauna
Karku ce ina da sanka kai
Ku yan uwa
Ba abunda zanyi ba kai
A rayuwa
In na tashi naga bakai
Da damuwa
Duk macen da batada irin kai
Tana ruwa
Nidai nasamu nau nayi hayewa
Allah ya bani ba yin kaina
Maya ke nake wa soyayyata
Zuciya dake kadai tai yarda
Kaine pillow na barcina
Inda rayuwa
Kaine abun tinani
Mai kore damuwa
Suna tayani murna
Dangi da yan uwana
Idan kazam mijina
Kowa yabar gurina
Kai kadai naba gu zo zauna
Kaine a zuciyata da raina
Maya
Nice mai kaunar ka
Maya
Nice zan aure ka
Maya
Na shirya zan bika
Maya
Written by: Arewa Medium Production