Top Songs By Abdul D One
Similar Songs
Credits
KOMPOSITION UND LIEDTEXT
abdulkadir tajuddeen
Songwriter:in
Lyrics
Ya mama, ya mama, mahaifiya
Soyayyarki mama, ta cika zuciya
Tunanina ran da zaki wuce ki barni mahaifiya
Ko ni in wuce in barki a zaune cikin duniya
Wayyo Allah wayyo Allah, dubi mahaifiya
Kasata cikin aljanna dan khairil anbiya
Wasu sun wuce tun kafin zuwanmu duniya
Wasu sunyi hakuri na rashin mahaifiya
Toh ga namu raye,me zaya sa baza mu kyautata ba
Ohhh, haba abokaina
Iyaye sunada matukar amfani
Da dukka ba wande ke a raye duniya
Iyaye
Tun kafin haihuwa suke yawaita dawainiya
Wayyo mama, mama wayyo mama
Zauna lafiya, mamana me sani dariya
Zauna lafiya, uwata mai ban kashin miya
Zauna lafiya rabin jikina mama uwa daya
Allah sarki uwa, mai dauke damuwa in bake ba lafiya
A rashin uwa wasu ke rasa sashin jiki gaba daya
A rashinki ne wasu ke koma yin bara su zagaye duniya
A rashinki ne yaro a gida yake zama maraya
Naga illar rashin mahaifiya kusa dani wayyo ni
A sanadin hakan nake kiran uwane na na cikin duniya
Ku daure, komai iyayenmu maza za su maku ku jure
Fitarku kubar gida na haifar da babbar hatsaniya
Wayyo iyaye kune tushen gida da zaman lafiya
Zamanku tare da 'ya 'yanku na kara dankon soyayya
Sannan zasu samu tarbiyya, ko ina zasu zauna lafiya
Sabanin hakan zasu kauce hanya madaidaiciya
Bana wasa da mamana, kaima kar kayi wasa da mamanka
Domin itace farincikinka duniya gaba daya
Uwa mai kula da dandanta a kowane hali bazata barshi ba
Babbar sarauniya da tafi kowace a duniya
A kanku ne nake batu iyaye mata gaba daya
Ku sanya hakuri cikin gidanku ku zauna lafiya
Mama, mama, wayyo mama
Mama, mama, wayyo mama
Mama, mama, wayyo mama
Written by: abdulkadir tajuddeen