Lyrics

Ahhh Tururu-rururu Lalala-lalala Akwai bayanai wanda na tanada dan cike buri Amma ki shaida ba zan ki kiba ko a labari Akwai bayanai wanda na tanada dan cike gurbi Amma ka shaida ba zan ki kaba ko a labari A bayanin farko, kaine hasken da mai rabarka A misalin farko, kishi na bai bari wata ta kushe ka Tunda ka zama bango, rabarka sai ni kadai matarka Tausayi da kulawa, nice na dace na kwanta kirjinka Ruwan guban 'yanmata ko sun sha haka zasu amayo ka Muyi gaba kar muyi baya, fushi ko fada babu tsakaninmu Ahhh babu tsakaninmu Cikin dabaruna,zanyi kalamaina domin su birgeki Cikin bayananki zanyi aron baki domin in tsumaki Cikin lissafina zanyi karanbani na ko zana cinyeki Inasan kin bani aran hankalinki dan zani saita ki Ganinan zuwa gidanku da sako (ohh yeah yeah) Kullum tunaninki nake budar baki harma daren baccina Ahh ni bana komai, bana kula kowa Ba kai wa zan gano, har inyi yaba Karkon menayi ma, ba'a misaltawa Dan shiyasa ma ba'a kwatantawa Haka karkon so yake a zuciya sai an daurewa Ni nayo sa'ar nawa, lallai bana kuka Ahaa Ni ko makancewa nayi, ban barin sonki Ko kurma ne, ni bani kyaleki Kyakkyawar sura, kin wuce sarki Allah ya tsara, zan zamo naki Dan Allah kar ki gujeni Kar ki barni in sha wahala Ki amince kece zaki bawa zuci gurin kwana
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out