Lyrics

A gidan sarauta
Sarauta, sarauta
A gidan sarauta
Dake zan daura aure
Ki zamo sarauniya ta
Kaine jarumi na
Da kai zan daura aure
Ina rokon Allahu Sarki
Kare mu sharrin masu baki
Yaye kunci ka bamu sauki
Soyayyar mu ta kara zaki
Hanya mun dauka
Bama son sauka
Zamu bi zabin ka
Allahu komai kayi daidai
Rabon ka naka ne bamai tsaidawa
Hukuncin Rabbi shi ba mai sauyawa
Komai ya iya, baya kasawa
Komai na bar masa, sai nayi dacewa
Yau murna ta
Na zama mata
Zanje nayi bauta na cika burina
Da mafarkin ki nake kwana barci
Da tunanin ki nake tashi barci
Da kalaman ki suke kore kunci
Daga kallon ki idanu ke sanyi
Da mafarkin ka nake kwana bacci
Da tunanin ka nake tashi bacci
Da kalaman ka suke kore kunci
Daga kallon ka idanu ke sanyi
Na gamsu dake
Na zabe ki ke
Aure zanyi dake
In saka ki a fada ta
Lallai na tsallake
Don an bani ke
Na samu sake
Zan nuna bajinta ta
Tunda kika ce masu sai ni
Ba zani saki kuka ba
A kan ka bani jin kunya
A ce na haukace a soyayya
Samun irin ka kwai wuya, a'ah
Wannan zamani duniya
A kan ka zan yi komai
In bada rayuwa ta
Dake zan daura aure
Ki zamo sarauniya ta
Kaine jarumi na
Da kai zan daura aure
Written by: Maishadda Global Resources
instagramSharePathic_arrow_out