Lyrics

Sultan
Auta Waziri kuke ji malam
Kece aljannata duniya
Masoyiya, aminiya ta
Kece aljannata duniya
Masoyiya, aminiya ta
In dai kika barni sai na sha wuya
Sai na zam kamar tsokar da babu jijiya
In ba dake ba sai dai rijiya
Rijiyar ma mai dauke da kugiya
Wacce zata caki rai na, ban kara kwana
Mai zai sa in kwana? Ban gano masoyiya ba
Kece aljannata duniya (aljanna)
Masoyiya ta, aminiya ta
In har zaki gita sai naji alama
Dan son ki ne shi ke kara bani himma
Kinga so dake nayi bani ba nadama
Ciwon da yake zuciya ne kinka fama
Kece kika gano ni koh a dukka mata
Karki bani rata dan koh baza ni kai ba
Kece aljannata duniya (aljanna)
Masoyiya ta, aminiya ta
Ki sani komai nisan, nisa baza na barki ba
Baza na dauki watan ki in ijiye ta a daki ba
Dan ba da sunan ta na gina wannan sashin ba
Kwado da makuli ina binki kamar baki bude ba
Banji ina kyarar ki koh na dakika ba
Na san soyayyar mu dake baza fah ta goge ba
Kece aljannata duniya (aljanna)
Masoyiya ta, aminiya ta
Mafarki na baza ya tabbata ba
In ba auren ki kawai nayi ba
Tunani na bazai kyar kyata ba
In har baza ki yi nisa ba
Na san so na da dadi
Mai yin sa kan ji duniya da fadi
Wani sa'i ya sa ka kuka
A Jarumi kai kada ya fadi
Ni na daina fargaba
Dan na san baza na barshi ba
Kece aljannata duniya
Masoyiya, aminiya ta
Sultan with the beat baby
Written by: Auta Waziri
instagramSharePathic_arrow_out