Lyrics

[Intro]
Musax
Musax Mix
[Chorus]
Ki yi da ni
Ke ɗaya ce nake gani cikin idaniya na zuciya ta samu salama (Ki yi da ni)
Rai da zuciya gabaɗaya ke kaɗai suke ta nema (Ki yi da ni)
Duk idanuwan da suka gan ni tare ni da ke cikinsu za ni ƙara ƙima (Ki yi da ni)
Kin mallake komai, a kanki yanzu dole za ni ƙara himma
[Verse 1]
Na ba ki duka mallakina
Ko da a zuciyarki za ni ƙara girma (Ki yi da ni)
Zan ɓata duka lokacina
A son ki ba na jin da za na yo nadama (Ki yi da ni)
Gare ki ke da ra'ayina
A kanki ba ni shiri da masu yi mi ni gulma (Ki yi da ni)
Alkwari riƙe min
Kada ki sake min
Ba ni bar ki ni ma
Alƙawari riƙe
Kar ki yo sake
Ba ni bar ki ni ma
[Bridge]
Ki yi da ni
Ni dai ki yi da ni
[Verse 2]
Halinki ya yi (Ya yi)
Zubinki ya yi
Na faɗa masu komanki ya yi (Ya yi)
Komai za a yi
Ni dai dole yabo sai na yi (Na yi)
Na-na-na-na-na
Haka yake, haka yake
Ƙalbina ban aje kamar ki ba
Komai nake, ba na sake
Idan idanu ba su gan ki ba
Inda kike, a nan nake
Ina da tabbacin ba zan faɗi ba
[Verse 3]
Wallahi tallahi
Ke za ni kai gidana
Wallahi tallahi
Ki ɓoye sirrikana
Wallahi tallahi
Kin zam jinin jikina
Wallahi tallahi
Ɓargon cikin ƙashina
Wallahi tallahi
In ba ke babu raina
Wallahi tallahi
Babu lafiyana
Wallahi tallahi
Ki zama mallakina na har abada na cika burikana
[Outro]
Wallahi tallahi
Mix
Musax Mix
Written by: Sadiq Saleh
instagramSharePathic_arrow_out