Top Songs By Hairat Abdullahi
Credits
KOMPOSITION UND LIEDTEXT
Hairat Abdullahi
Songwriter:in
Lyrics
Salim Smart on the beat
Idan na ji an fadi kalma ta so
Hawaye na zuba suke
Bana bukatar in sake dandana shi
A guna guba yake
Na rasa gane dadin sa
Ni kamar chi min diddige yake
Yaushe sa'a ta zata kama so?
Dadin shi in sanni
Ko yaushe sai duhu, haske bai zuwa ido na
Ko da na hau tudu, ban hangen farin ciki na
Sai makuwa nake yi soyayyah tana bugu na
Bana ganin gabas balle in san inda zani
A cikin jarabawa ta so ne kan gaba
Shi ke wahalar da ni
Yayi mani tambun, kowacce gabar jiki
Ya nakasar da ni
Ya sa mani wasi-wasi a zuciya
Tuni ya batar da ni
Na rasa gane so daya na gaskiya
Wanda zai kulla da ni
Dama zaka barni, bazan so ka ba
A da nayi so da kai, ban ji dadin sa ba
Ni ban san bayani, dan bazan ji ka ba
Bazan karbi uzurin ka ba ni ka manta da ni
Soyayyah, na barta na daina
Na huta, babu kowa cikin rai na
Na manta, da kai kar kazo guna
Na yafe, so da kai bani sakewa
Written by: Hairat Abdullahi