Featured In

Credits

AUSFÜHRENDE KÜNSTLER:INNEN
Isa Gombe, Mubarak Dutse & Farouk M Inuwa
Isa Gombe, Mubarak Dutse & Farouk M Inuwa
Künstler:in
KOMPOSITION UND LIEDTEXT
Nura M. Inuwa
Nura M. Inuwa
Komponist:in
RR
RR
Songwriter:in

Lyrics

[Verse 1]
Har zuciyata na aje ki
Komai wuya ni ban barinki
So na fada ba ki da ba ki
Ce nai ki so ni don ma'aiki
[Verse 2]
Ba don kudi ba koko mulki
Duba jiki na babu kakhi
Ke na gani cikin mafarki
Har na aje kudin sadaki
[Verse 3]
Don na gujewa masu tsaki
Zan ta dawainiya da sonki
Dadi wuya ni ban gudunki
Tunda a so nine ajinki
[Verse 4]
Baki yana yawan kiranki
Burin idanuwa ganinki
Za na kawar da masu kinki
Na yaba dukkanin zubinki
[Verse 5]
Za na kiyaye martabarki
Na kidime ganin dirinki
Kallo guda na yo a gunki
Na rikice da kyan sufarki
[Verse 6]
Kalarki ta wucewa tsaki
Dole na so farin cikinki
Aurenki shi nake ta doki
Akwai abin da ban fadanki
[Verse 7]
Ki tabbata ina jiranki
Na zama kamar soko a kanki
Sai yaushe zan hau karagarki
Duk inda za ki zan raka ki
[Verse 8]
Ni ba ni so ki dinga raki
Gunki na zam kamar sadauki
Ban kyale wani ya taba ki
Domin na dubi fara'arki
[Verse 9]
Dai-dai ki tattaka kafarki
Don kin zamo diyar saraki
Nai tambari nake yaba ki
Kwai kyalkyali a sutararki
[Verse 10]
Na waiwaya ga tarbiyyarki
Ba na tsana kin hau tafarki
Iyaye naki sun hada ki
A kasa ban nufin na ja ki
[Verse 11]
Da haka ne ni ban kula ki
Jigo zan zam a rayuwarki
So na na zamma ginshikinki
Ki so ni babu dole gunki
[Verse 12]
Na san kina da masu sonki
Zabi guda ki sa shi ranki
Amma ki yi nazari da kanki
Ki dauki mai tsare hakinki
[Verse 13]
Wannan da ba shi tawayarki
Ki kyale masu bibiyarki
Ware guda ya zam gwaninki
Nan gaba zai yi tallafarki
[Verse 14]
Shi zai guje bakin cikinki
Ya ga ruwa cikin idonki
Duk hankalinsa zai yi gun ki
Wani ko so yake ya wanki
[Verse 15]
Kuruciyarki a mataki
Idonki ya zuba hayaki
San da ruwa ko ya jika ki
Sai ya ji ba shi ra'ayinki
[Verse 16]
Har ya ji ba shi son kula ki
Ya sallame ki bai tuna ki
Ya girke baya yanzu ga ki
Don tsufa ya disashe kyanki
Written by: Isa Gombe, Mubarak Dutse & Farouk M Inuwa, RR
instagramSharePathic_arrow_out