Lyrics
Eh jimami zanyi idan ka tafi, kai duban yanayi
'kauna ta bayyana so a jiki, koda babu kama
Eh nan ni zanbarki kawai na tafi, amma dai ki kula
So ya bata bayyana hali ba kenan babu kama
Ba kanwa baya da 'kura aiki bai tabbata ba
Sai kuka ran rabuwa da masoyin da kaba ragama
In ka tafibyau ka rabu dani waye zana rika
Na shakubdakai rami na mugunta ni bani haka
'dannan da mukai haifa a gaba zaiyi rashi mafaka
Ko ba dan ni ba dalilinsa karkaiyi gashi na kuma
Ba kanwa baya da 'kura aiki bai tabbata ba
Sai kuka ran rabuwa da masoyin da kaba ragama
Eh kamci na kaba dik mai nema nai zai sha wahala
In babu ido ba'a iya gane hasken fitila
Aikin 'daya ne ba banbanci yin nazari da kula
Nasan kin gane bayanin nan da nayi cikin hikima
Ba kanwa baya da 'kura aiki bai tabbata ba
Sai kuka ran rabuwa da masoyin da kaba ragama
Eh so yayiman mugun kamu yasanyani yabo
Shi yarda ka a fili har mun samu rabo
Tsammani suke har in bakai kaga hanin sabo
Nazo da shirin aiki amma gunka nasau ragama
Ba kanwa baya da 'kura aiki bai tabbata ba
Sai kuka ran rabuwa da masoyin da kaba ragama
Ba kanwa baya da 'kura aiki bai tabbata ba
Sai kuka ran rabuwa da masoyin da kaba ragama
Eh in angina soyayya da nufi to da akwai wa'adi
Raminna kurege akwai 'kofofi marasa adadi
Zafi maki kyau rabo dani ki neman madadi
Ko dan zaki a 'kyale rina ai zabe na zuma
Ba kanwa baya da 'kura aiki bai tabbata ba
Sai kuka ran rabuwa da masoyin da kaba ragama
Eh so lallai babban ciwo ne da ba'ai mai fahari
Ya bata man dukkan tsari gani cikin hadari
Ko ka tafi zana rufe sirri naima al-'kawari
Amma kudirinka akaina shike sanyani tsuma
Ba kanwa baya da 'kura aiki bai tabbata ba
Sai kuka ran rabuwa da masoyin da kaba ragama
Eh kyan 'da inji masu kari na magana yai gado na uba
'Dannan ki rike na baki amana ni nayi gaba
Akwai rana zana bukace shi indai ban mutu ba
Fata na dai ki mai horo yazama mai azama
Ba kanwa baya da 'kura aiki bai tabbata ba
Sai kuka ran rabuwa da masoyin da kaba ragama
Eh jimami zanyibidan ka tafi, kai duban yanayi
'kauna ta bayyana so a jiki, koda babu kama
Eh nan ni zanbarki kawai na tafi, amma dai ki kula
So ya bata bayyana hali ba kenan babu kama
Ba kanwa baya da 'kura aiki bai tabbata ba
Sai kuka ran rabuwa da masoyin da kaba ragama
Lyrics powered by www.musixmatch.com