Credits
KOMPOSITION UND LIEDTEXT
Sadiq Saleh
Songwriter:in
Lyrics
Sadiq Saleh
M. Shareefi
In kika barni kwarai lahira za tayi bako
Zo ki amshi makullin zuciya ki garkamo kwado
Duniya za tayi dadi baki na zamo fanko
An kira ni da "Sha-sha-sha" a kan ki na zamo lado
Ba bana ba tun bara
Kaunar ki zuci na ta tsira
Ke kinka mini dashe ina son ki
Don ke na ma rayu
Mance da taro na yu-yu-yu
Ko sun zo kice masu nine masoyin ki
Kinsan da sirri na
Kin boye baki taunawa
Assalam alama bana so alal hubbu ya habibati
Yarda
Na yarda dake (shine yake dada soyayya yarda)
Na yarda dake baby na (shine yake dada soyayya yarda)
Na yarda dake (shine yake dada soyayya yarda)
Na yarda dake baby na (shine yake dada soyayya yarda)
M. Shareefi
Lissafi na daidai ne
Kowa ya gane
In dai aure ne, ke nake zance
Da na dauke ki fam-fam-fam
Za na rike ki kam-kam-kam
Bani sake ki sam-sam-sam
Ki zo ki duba
Kaunar ki tayi min laga-laga
A zuciya tayi raga-raga
Cikin rai tayi mini daga-daga, daga-daga, daga-daga
Kyakkyawar yarinya ce
Mai ilimi mai kunya ce
Gun daraja zinare ce
Gashi dake zan angonce
Karshen kauna
Na yarda dake (shine yake dada soyayya yarda)
Na yarda dake baby na (shine yake dada soyayya yarda)
Na yarda dake (shine yake dada soyayya yarda)
Na yarda dake baby na (shine yake dada soyayya yarda)
Shine yake dada soyayya yarda
Soyayya yarda
Lyrics powered by www.musixmatch.com