Credits
KOMPOSITION UND LIEDTEXT
SANI AHMAD
Songwriter:in
Lyrics
Al'umar arewa
Hausa-Fulani
Arewa
Al'umar arewa ta
Arewa, al'umar arewa ta
Arewa, al'umar arewa ta
Arewa, al'umar arewa ta
Wayyo Nigeria ta
Al'umar arewa ta
Arewa, al'umar arewa ta
Arewa, al'umar arewa ta
Arewa, al'umar arewa ta
Ai yanzu dai al'umar arewa
Ba mai ta cewa
Ku tai nayo mutan arewa
Ake kashewa
Nigeria babu mai hanawa
Cikin arewa
Toh meyesa daga mutan arewa?
Ake kashewa
Cikin kasar nan
Wai me mukai ne?
Al'umar arewa
Arewa, al'umar arewa ta
Arewa, al'umar arewa ta
Kaduna ce cibiyar arewa
Yanzu an rufe ta
Zamfara noma muke arewa
An saka mu bauta
Katsina ta rikice arewa
Yau tana kanta
Sokoto sun samu matsaloli
Ya kode misulta
Mace da goyo tana gudu
An kashe mijinta
Babu ga babbah babu ga yaro
Dan kawai mugunta
Ya aka mai Nigeriar nan
Mu mutan arewa
Arewa, al'umar arewa ta
Arewa, al'umar arewa ta
Mu ka duba a Niger nan ma
An kashe arewa
An hana noma an hana kiyo
Tattalin arewa
Ga makarantun cikin arewa
Dukka ana rufewa
Yan Kebbi na wai waye su suma
Ba a abin tabawa
Babu dare kuma babu rana
Arewa hanya ake tarewa
Wasu su ce, "Matsalar Fulani"
Wasu su ce, "Matsalar Hausawa"
Fulani ai asalin mu guda ne
Mu a cikin yankunan arewa
Hausa-Fulani arewa zan so mu gane juna muke kashewa
Arewa, al'umar arewa ta
Arewa, al'umar arewa ta
Arewa wai ba sarakuna ne?
Kokuma ba masu magana ne
Arewa bama da malamai ne
Kokuma bama da gwamnatin ne
An ci amanar mu yan arewa
Ga jama'ar tamu nan tsugune
Mun rasa komai mun rasa kowa
Garin mu an kar kashe mutane
Babu abinci ga talakwa
Gashi a nai mana kone-kone
Babu dare kuma babu rana ana kisa mufa yan adam ne
Zubar jini ya zamo sana'a a yankunan namu
Me yasa ne?
Allah wadan dukkan shugabanin da suka zalunci yan arewa
Arewa, al'umar arewa ta
Arewa, al'umar arewa ta
Ga sodojin mu an kashe su
Ga yan sandan mu an kashe su
Ga likitocin mu an kashe su
Asibitocin mu an rufe su
Ga makiyayan mu an kashe mu
Dabbobin nasu an rike su
Gashi manoman mu an kashe su
Gonakin babu mai kula su
Yan kasuwar tamu an kashe su
Ga kasuwar nan ana gudun su
Ga malaman mu an kashe su
Ga makarantun mu an rufe su
Direbobi ana kashe su
Matafiya kuma ana rasa su
Allah sarki mutan arewa
Wayyo ni mutumin arewa
Wani mahaifinsa yai rasawa
Wani ko innar sa yai rasawa
Wani ko matarsa yai rasawa
Wata mijin nata tai rasawa
Ga wata ta rasa saurayi
Wani budurwarsa yai rasawa
Wani koh ya rasa kowa da komai
Duk sanadin rikicin arewa
Allah kai kai mutan arewa
Masu kudi harda tallakawa
Ka kawo karshen fadan arewa
Allah kai muka roko
Arewa, al'umar arewa ta
Arewa, al'umar arewa ta
Al'umar arewa
Hausa-Fulani
Writer(s): Sani Ahmad
Lyrics powered by www.musixmatch.com