Lyrics

Gangar kidan na manyan mata ne Sannan batun da zan na iyayye ne Breaker akwati mai zance ne Inji Tariku medium na sarkin waka Ya Allah dafa min kasan baza na iya ba Ya mai iko kai ke kyautar da baka karba Ya sarkin mulki bani yau na zazzaga zance Yau wakar ta iyayyen da basuyin rowa ce Ma'ana ta iyayyen amarya kunji karshen zance Masu kyautar 'ya in nayo kuma hadiya ce Ya rabbi ka linka salatin daha karshen-karshen Sidi gatan kowa kaji farkon tushe Mai kafa musulunci sansani kawai dacewa Maman amarya fito na baki babbar ganga Kin san dolle na maki taho da takun burga Maman amarya fito na baki babbar ganga Kin san dolle na maki taho da takun burga Kin kai a yaba maki uwar dawa kushewa Mamana abun biki nake dubawa Na ganta a zaune a rai nadin ta na sukawa Idan na tuno ta haifi yarta zasu rabewa Sai inji tausayi na mama ya kama ni Ku tuna daukar ciki da haihuwa sai mama Ku tuna raino zama cikin uwa sai mama Ku tuna jure kiriniya diyya sai mama Mama sannun ki a jinjina wa mai alfarma Mama kenan sanar dake abun birgewa Ke kika zamo farin wata dake haskawa Tarbiya 'ya'ya mama ke ake kangawa Mama mai hakuri gani yau cikin fadar ki Yau nai aniya na zage dantse sai na gaida ki Sannu uwar amarya ga jinjinata gun ki Salisu yaro dauki alqalam ka rubuta Komai na fada sai yazama ka nanata Tafiya da gwani dadi gareshi ga kalmata Yau dai uwar amarya nakewa waka ta Yanzu mahaifin amarya zana komo gunka Wasu baituka ne na girma zana miko gunka Ka kai a yaba maka da hikima san barka Kaga maza, jiya zaki fama mai yiwa kowa Amarya ki duba ga mahaifi naki yana ta yin rawa Buri nai a fita kunya na gaida kai baba Kafin ayi murna baba yana darawa Mun sha aiki (jinina alfarma) Baba an sha aiki (jinina alfarma) Mai girman mulki (jinina alfarma) Shi ai jirgin ki (jinina alfarma) Tudun kan tafki (jinina alfarma) Yau nayi maka marki (jinina alfarma) Yaki gama aiki (jinina alfarma) Duk kundar kirki (jinina alfarma) Toh amaryar gareki (jinina alfarma) Yau dai sai an kai ki (jinina alfarma) Share kukan ki (jinina alfarma) Inji baba ya ce in sanar maki (jinina alfarma) Zama na gidan ki ki dan rike (jinina alfarma) Mama gare ki na dan kake (jinina alfarma) Na kawo tsaraba ga ke (jinina alfarma) Dake da mijin naki (jinina alfarma) Har bude murya nake (jinina alfarma) Wani taku dai nake (jinina alfarma) Har wani taku dai nake (jinina alfarma) Sai wata rana (jinina alfarma) Na barku yan uwa na (jinina alfarma) Amman ga sako na (jinina alfarma) Mama ina nan zan kuma dawowa Ga jinijina mai girma Ga jinjina alfarma
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out