Lyrics

Nagode Al'umma nagode Zan fada muku nai godewa Na nara yi muku godiya Matan ku da mazan ku Nura ne M Inuwa Gani ina nai baitin godewa Ku fada nagode Ban raina abinda kuke tayi mini ba Mun gode yan uwa Kun soni da riba wace babu riba Mun gode Burinku a koyaushe ku ganin ni gaba Mun gode yan uwa Na gaskata kyawun 'da ya gaji uba Mun gode Na rike gado kunga ban bata ba Mun gode Uhmm-mm-mm-mm-ah Jirgin sama dan Allah ka kaini gari Mun gode yan uwa Naje nagano jamma'a ta Maiduguri Mun gode Da yankina na Arewa zan fahari Mun gode yan uwa Masoyan annabi masu yin zikiri Mun gode Kanawan Dabo suna da alkawari Mun gode yan uwa Basu cuta walla suna sakan sumari Mun gode Zancen zaki sai an sako sikari Mun gode yan uwa Wajen ta'adi bera ya gaji bari Mun gode Katsinawan Dikko gari guda ya dari Mun gode yan uwa Baku tsoro don kunya kuke uzuri Mun gode A zama da shiri feshi kukewa sari Mun gode yan uwa Kaduna garin gomna nake nazari Mun gode Haske ya kore duhu kuna sarari Mun gode yan uwa Da sara gamji bazaya je kasa ba Mun gode Da alamar karfi naga masu kiba Mun gode yan uwa Gashin tsire sai dai akan tukuba Mun gode Wanda zashi Abuja zaya iske zuba Mun gode yan uwa Babban birnin Najeriya nasaba Mun gode Yan Niger bazana naki in yaba musu ba Mun gode yan uwa Mai tafiya aka so ganin tsara ba Mun gode Dutse tsawa bata saka shi layi Mun gode yan uwa Da hazo a alamomin chanjin yanayi Mun gode Yan yobe mun zauna ne akan ra'ayi Mun gode yan uwa Domin marar ji akace jiki magayi Mun gode Dan kare da biri haduwarsu ya akayi? Mun gode yan uwa Watan zafi acikinsa ba'a rufa Mun gode Baushen daya kai yawo yake da kwafa Mun gode yan uwa Aiki ya kaini Jigawa sau da kafa Mun gode Tarin Allah yaransu basu dufa Mun gode yan uwa Tabbas da gani aka dadale harufa Mun gode Zamfarawa suka rabe ali da kashi Mun gode yan uwa Sun bani tuwo da miya cikin akushi Mun gode Mai hakora ke tautauna tantagwashi Mun gode yan uwa Indai da akwai suya a kyale gashi Mun gode Yan Sokkoto kan fuskarsu babu fishi Mun gode yan uwa Birnin Shehu san kowa hakkin marar shi Mun gode Kan alkawari aka sanki tantabara Mun gode yan uwa Suga ta biki aka yin kiran amara Mun gode Ruwa sai ya zuba kan hatsi ya tsira Mun gode yan uwa Kabawa idan zakuyi baku jira Mun gode Yan kebbi kalar nono kalar madara Mun gode yan uwa Iska ita dai ce ke tsayar da gumi Mun gode Tarin falala sai dai watan azumi Mun gode yan uwa Mutan Adamawa dasu na dau harami Mun gode Yayinda na dau waraqa da alkalami Mun gode yan uwa Kunga Gombe na zazana a da'ajami Mun gode Gombawa kune dai akan kadami Mun gode yan uwa Lissafi ne yasaka nasan adadi Mun gode Ajali in yazo an ishe wa'aadi Mun gode yan uwa Taraba jihar nan bata da madadi Mun gode Ance da rawa basa wuce makadi Mun gode yan uwa Jama'ar Nasarawa basu jin radadi Mun gode Na gansu cikin bana alo kai mu badi Mun gode yan uwa Yan Kogi hakika basu nuna issa Mun gode Yan Plateau kofata suna kwankwasa Mun gode yan uwa Giwa tai rasa bata cin dusa Mun gode Kwara a jihohi ta wuce gasa Mun gode yan uwa Benue ma guna sun wuce kusa Mun gode Har Bauchi garin masa nake dosa Mun gode yan uwa Dan dole ruwa a so shi bai ginsa Mun gode Baitin kauna na biyo shi Ba wasa, nagode ku fada Mun gode yan uwa Nagode Mun gode Ku fada Mun gode yan uwa Ku fada Mun gode Nagode
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out