Lyrics

Bakin duhu ba haske Ganin sa ma hadari ne Dafi na so nayi kangabo Gun sa na tunkara Dafi na so akwai zafi komai kankanin sa Yafi dukan dafin kwarayar dandano Dafi na so akwai zafi komai kankanin sa Komai kankanin sa Mamallaki, mabuwayi ga kai na taho Roko gare ka nazo nasan baka maho Sai dai mai yin halin dabba mai kaho Da kunyi nasha azabar dandano Komai kankanin sa Da so tazo gare ni Tazo a gare ni Ruwan guba ta bani Kishi ta bani Nasha guba ta madara Ina a ban kunfa fara Gumi yana kwarara Ina zubar da dahara Aman jini yazam mai bi a baya Domin soyayya ta saka riga ta karya Da so tazo mini Ma'ana, ta mato mini Hidima take mini Ragama, ta sakar mini Bata so mu samu sabani Da haka zuciyata tai rauni Har sai da son ta yayi min rauni Daga haka sai na zama a rudani Zafin so a zuciya ta na dafa ni Gashi ashe tana da aure na gano Zafin so a zuciya ta na dafa ni Gashi ashe tana da aure na gano Sarkakiya ta so cikin gurbin wuta Ta sani can sakan tala na rasa mafita Gurbi na zuciya ta Kamar ana dafa ta So yaki diddiba ta Zai tsaida duk bugun ta Tillas na barta don guna ta haramta Matar wani gubar wani na fahimta Na barta ammah son ta na karan jigata Aman jinin bakin ciki ya bayyano Ya bayyano
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out