Lyrics

[Verse 1]
Maimuna gimbiya ina baiwar Allah
Dadin duniya kina nan da kamala
Giwa ko ana matsi sai kin wala
Maimuna mun yabe ki mai jimirin sallah
Maimuna ba musu irin ƙila wa kala
[Verse 2]
Maimuna kin kula da sunnah da farilla
Maimuna bangaren zumunci mu'amalla
Maimuna ce babba 'ya gun babba
Mai halayen kwarai mun duba
[Verse 3]
Maimuna hasadar magauta zama taki
Maimuna kin ji kin ji jita ta kira ki
Maimuna taimakon mutane a jininki
Maimuna ki ta kwaliya ga kayanki
Maimuna kinyi kyau a mota haka doki
Maimuna dole zana fassara sunanki
Mai albarka a dan dudduba
Larabci ne ba zamu ki yi ba
[Verse 4]
Wannan tamburan muna yinsa ga maimuna
'Yar birni tana ta turanci maimuna
Mai hakuri tana da imani maimuna
Ji da ado adon gari kece maimuna
Mai kamshi a kodayaushe ce maimuna
Kunshi yafi kyau da hanayyen maimuna
Zaga gari baiwar Rabba
Nasarori ai ba sa kare ba
[Verse 5]
Mai tafiya kazo da sako in ba ka
Ga jita tana ta tashi sam barka
Ga yara suna rawa 'yan albarka
Ga manya suna ta girgida kai hakka
[Verse 6]
Allah yayai ruwa manoma na shuka
Ko ni ya kamata wakar in taka
Wakar maimuna bazan fasa ba
Maimuna ai kina da suna babba
[Verse 7]
Ki yi shagalinki duniya a amfana
Duk dangi da yan uwa kowa murna
Sannan lafiya da kowa kin zauna
Har aljanna za ki aiki ya nuna
[Verse 8]
Maimuna gimbiya da kyauta da amana
Kuma kuka na duniya sai kin daina
Yar manya matar manya
Nasarori ai ba sa kare ba
Written by: Ali Isah Jita
instagramSharePathic_arrow_out