Lyrics

[Verse 1]
Sarauniya ta boye, takenki zan yi yanzu
Wa zai tsananta kallonki yanzu ijiyarshi ta tsiyaye
Kullum ina faɗa na kara cewa kina a raina
Sam ba ni mance alkhairinki don yai yawa a gu na
[Verse 2]
Ƙaunarki kin dasa min 'ya'yanta sun yi huda
Ba zan shiru ba nima a kanki sai an kira ni suda
Kaunarki ta yi dadi garen ya zakin icen takanɗa
Kin haƙa rijiyar sonki ta yi zurfi ciki na faɗa
Ba za na gane kai na ba sai kin zamon icen ƙirya
Ba na faɗi ba ne tunda komai a kanki na shirya
[Verse 3]
Ina son ki so na haƙiƙa da ke mu hau hanya
Idan kina tunani na ina na ki ne cikin duniya
Ni ɗin ga na ki ne in babu ke a kira ni da maraya
Ina yawan faɗar a kanki nake kara kyauta halayya
Kin ji masoyiya
[Verse 4]
In babu ke cikin duniya ina za na je ni don kwana
Ɗan dakata idan kin jiyo ni ban son ki furta bankwana
Sirrin da ke tunani na ba ki ni zan riƙe ki da amana
Ko ban yi miki daidai ba
[Verse 5]
Ni dai kawai abin da na sani ina sonki tun da na gano
Ke ma ki furta kin yarda ban son na dinga bonono
Kowa yana fadar ke kike gu da an ga na kunno
Mai kyan sufa da kyan haiba
[Verse 6]
Ke ce adon gari tun da kin saba zarta 'yan mata
Sannan sinadarina da na bar ki wallah nai wauta
Ke nai wa tanadina cikin duniya ina fata
Ki ce ba zan yi rauni ba
[Verse 7]
Ina yawaita zancenki ba na dare bare rana
Ki tausaya garan kar ki bar zuciya cikin kuna
Na san kina sane tunda na bayyana tunanina
Mai sonki nake 'yar baba (Midget Mix)
Written by: hamisu said yusuf
instagramSharePathic_arrow_out