Top Songs By Hamisu Breaker
Similar Songs
Credits
KOMPOSITION UND LIEDTEXT
hamisu said yusuf
Songwriter:in
PRODUKTION UND TECHNIK
Kasheepu
Produzent:in
Midget mix
Mastering-Ingenieur:in
Lyrics
Beats Amjad Records
Ashe da rai nake sonki jaruma ba da zuciyata ba
Komai ruwa da iska a kanki ba za daina kewa ba
Idan na samu zarar samunki ba za na tanka kowa ba
Ni ban ga mai harara ba bare na wai ya ah
In dai a kanki ne za na jure wahalar zuwa garin nisa
Da an taɓaki a jira ni don ko tilas na zo na ɗau fansa
Jimirin jiranki nai don ki zo na kalleki gimbiyar Hausa
Sirri na rayuwata ke ce kawai da kin kira da na amsa
Zuma a baki daɗi gare ta kin ba ni ta ki na lasa
In dai a kanki ne na yi nisa don ba kiran da zan amsa
Tilas ganin mu tilas barin mu ƙaunarki tun da nai nisa
Sam ba batun nasa fasa ko za a ce mun in ba da rai fansa
Tsarin zubinki dai dai ne
Ya kama zuciya ta ne
Ina jin kamar mafarki ne
Ina sonki so mataki ne
Ni ban da damuwa in har zan buɗe yan idanuna
In kalle ki ga ki daf da ni to me za ya da ni ƙalbi na
Yauwa za na yo amo tun da na gane kina da tausaina
Don yanzu na zamo ya mafatauci mai biɗar gurin kwana
Na kwalla shela dan sanar da iya maƙiya kalamaina
Daga zuciya nake kwatanta ina zayyano jawabaina
Idan babu ke ina ne zan saka zuciya ta bar yawan ƙuna
Kowa da nasa amma ni ke ce cikar muradai na
Yau gani a ruwa kusa da kada zo ki ceci ƙarko na
Komai da mafuta kar da ki saba da furta ban kwana
Ina ji ina gani yadda nake sonki yafi ƙarfi na
Na san a duniya da wanda yake janye duk tunanina
Soyayya rayuwa wani saʼin sai tazama wutar ƙuna
Duk wanda ke cikinta shi ne jurau amma fa a wurina
So na faranta rai da ruhi yasa ka zama kamar sarki
Kuma rayuwa da so misali nai na kama da a mafarki
Samari mu yi hakuri idan har mun samu so mu sa sauki
ʼYan mata muyi hakuri idan har mun samu so mu sa sauki
Masoyi yana da rana ne
Masoyi yana da rana ne
<span begin="3:09.289" end="3:13.086">Masoyi yana da rana ne</span> <span ttm:role="x-bg"><span begin="3:10.072" end="3:11.268">(Midget mix)</span></span>
Written by: hamisu said yusuf