Lyrics

Hmmm, abokanai na taho da zance
Zan baku labari a takaice
Soyayya ance ruwan zuma ce
Na dandana naji ruwan guba ce
Nayi gamo wata yarinya ce
Kyakkywa zuciya ta sace
Na rasa ya zana yo kwatance
In zana surar ta kar na mance
Ta kai karshe gun kyau duniya ce
Cikin yan mata ko fitila ce
Ga dadin sauti
Ta iya zance
Kullum muna tare da maraice
Idan nace mata amarya sai tace
Kai kuma ango raina ta farance
Na shirya aurenta koda da rance
Don bani so wani ya mini kwace
Kullum tunani in nayi kwance
A daura auren mu kar na zauce
Ashe cikin ranta babu zance
Tasa abun sarkiya da kwance
An sanya auren su kuji zance
Mece dani kuce yaudara ce
So in ya zamo cuta
Ka dau hakuri shine magani
Nima haka nan na fafata
Soyayya ce ta koyar dani
Kuji kadan labarin ta
Halayya ce ta yan zamani
Muna soyayya ni da ita
Ta soni kamar ta shayar dani
Dangi basu so na da ita
Na nemi wa zai fahimtar dani
Sun bincika halayyar ta
Tasa niyya ta cutar dani
Sun hada baki da zabin ta
In an daura su kayar dani
Sannan su kwashe dukiya ta
Suyo aure su manta dani
Nabi a sannu takun ta
Na gane hakan ya rikitar dani
A zuci ta sakan cuta
Nai kuka da ido baji ba gani
Gashi nai nutso cikin son ta
Na dau hakuri ya warkar dani
Naji zance ku na tausaya
Amma kun sani fargaba
Hakin da kuka shiga a soyayya
Ni ko ban shige shi ba
Ina da wacce muke tarayya
Ta gaske mai ci gaba
Ko bani lafiya zatai jinya
Ba zata guje ni ba
Ku dauki hakuri kuyo dace
Ku sanya haka duk jarabta ce
Kowa akwai nashi a rubuce
Ba mai tsallake ta kaddara ce
Wadansu kuka cikin duniya
Wadansu sai dariya
Mai hakuri tare yake da Allah
Akwai ranar sakayya
Written by: Abdull D
instagramSharePathic_arrow_out