Top Songs By Nura M. Inuwa
Similar Songs
Credits
AUSFÜHRENDE KÜNSTLER:INNEN
Nura M. Inuwa
Künstler:in
KOMPOSITION UND LIEDTEXT
RR
Songwriter:in
Lyrics
Ehh manyan mata ni tamburan ku
A yanzu nake daka
Kuko yan mata aikin ku yau
Bai wuce rike jaka
Duniya dadi na lura
Babu kamarku uwa uba
Haka ne yasa
Nai muku yanzu rabar ku, ku rarraba
Yanzu ni waka nake yi
Wasu suji su fadi tayi
A fadin Hausa kama da wane
Bata zama wane ba
Dinkin hannu idan ka bani
Bazan iya yin shi ba
A cikin waka ta mata
Godiya zanwa uwata
Komai me zanai
Ni nasani bazana biyaki ba
Allah sarki yaja da ranki
Akwai kallo gaba
Wataran, ba wataran ba
Laifuka na nayi tuba
Ita kaisata
Tilas a kyalewa giwa tayi
Mai ciki ko babu nakuda
An san ta laulayi
Mai daka zai nemi turmi
Fito ruwa sai da komai
Ance kanwa uwar gami ce
Ban musu haka ba
Gashin tsire ba'a yin sa
Idan ba tukuba
Jini na chan a kwata
Yin fawa sai mahauta
Tinanina daban da naku
Idan nai nazari
Hanyar jirgi
Daban da mota fannin sufari
Tunda ba'a ado da yana
Shinge kare gidana
Ana kallo yau kallabi
Shi ke jan rawani
Cutar mutuwa sai hakuri
Bata jin magani
Lissafi sai kwakwalwa
Ga salwa ga makwarwa
Koh ba yanka kifi
Ana iya kamawa aci
Shi agogo
Akan saka hanu domin lokaci
Sammako ke sanya sauri
Noma a kwari da tauri
Yanayin danshi kesa jikin bango
Yayyo rima (yayyo rima)
Busa ta kaho da tai yawa
Yan maza sa hau suma
Da ganin haure katanga
Ansha wahala a daga
In zan hutu
Nakan bidar inyi bakin dausi
Allah sarki tsareni
Kar nayi kallon tsautsayi
Zafi ga dafin kunama
Maza sun kwaci gulma
A buga a bari amara kirjin biki
Sai mai daraja ake fadawa harkar arziki
Garwashi ya dauki zafi
Rijiyata tayi zurfi
Mu rike noma
Rufin asiri ne gun talaka
Mafaruci dan ya kare kansa
Yake daukar baka
Zakara in yayi chara
Ba'a jin kurwa ta kura
Kiwon shanu da karnuka
Ba'a kai fulfulde ba
Filin danbe sai masu karfi
Zaka gani gaba
Ranan a cikin mafarki
Naga na kayar da gwanki
A jikin kaza da yan uwata
Ake samun uma
In ga manya su yan kanana
Dole su salama
Hali baya kama da sufa
Takalmi yafi safa
Auduga ba sutura bace
Sai in an sarrafa
Nutsuwa ce zata rarabe
Mana zaki da kwafa
Korama dangin su gulbi
Ha'ka sai da magirbi
Ita rakumi tana sama
Tai nisa da kas
Akuya in za'a mata kora
Bata gane asas
Kamshi ya girmi wari
Bauri ya gaji bauri
In za'a yi gada a bari
Sai anje dandali
Na lura bakin jini ake
Gun karban gangali
Gatari aikin sa sara
A yawa aka samo rara
Indai kaji wahidi
Guri da akwai almajiri
Mata suke ta'anmali
Da siyan kayan yari
Wata ta kere wa tsara
Agurin wata ba dabara
Hadari in ya hado
Samaniya zakaji rugugi
Kallon kallo maza na daure
Sukan ce majigi
Gyada ta jure bara
A kwashi tuwo da mara
Manyan mata domin ku
Nai wakar nan na fada
Lyrics powered by www.musixmatch.com