Similar Songs
Credits
AUSFÜHRENDE KÜNSTLER:INNEN
Auta mg boy
Künstler:in
KOMPOSITION UND LIEDTEXT
Auta mg boy
Songwriter:in
Lyrics
AMG Boy
Ga amarya ga angon ta soyayyah
(Eh mana)
Toh ga amarya ga mayen ta an daura
Toh ga amarya ga angon ta soyayyah
Farin ciki ya karu sai murna
Rabbana nake yin roko
Ni bawan ka na dau koko
Ka taimake ni in kai sako
Ango amarya ga burin ku an daura
Farin ciki shikenan soyayya
Dubun salatuka gun manzo
Dan Amina baituka sun wanzu
Sa da Alihai Sahabbai yanzu
Wanda bin su shi nake ko yaushe, don Allah
Sanya baituka na suyi suna anfara
Toh wai amarya menene ne?
Gidan ki zaki je kiyi zaune
Auren ga naga alkhairi ne
Wallahi kayi dacen mata kai ango, da amarya ba rainawa kun dace
Ango fah kaga karshen zance
Amarya sai da ka tantance
Ka yowa yan samari kwace
Auta na MG mai waka ne, na shirya
Toh amarya ga wakata ga ango
Abin bida ashe ya samu
Ango amarya yau dai gamu
Mun zo baki kamar dangin mu
Taro na gaske taron kauna, ga ango ga amarya yau kunyi aure soyayyah
So ya hadaku alkhairi ne
Aure kukayi yau sunnah ne
Zaman da zaku yi sirri ne
A da kuna ta labari ne
Sai gashi kun shigo tsarin ne
Jiran jira ta kare muku an daura
Ku kadai ake nunawa a taron nan
Kyawun amarya ya kai karshe
Kota ko'ina ba kushe
Ango farin hakora washe
Ginin mahassada ya rushe, sai kunya
Ga amarya ga angon ta, an daura
Muna tayi ana nuna mu
Wadan su ko suna kushe mu
Bama tasu suje mu gamu
Tunda rabbi shi yasan kimar mu
Komai muke yana duban mu
Mu masu son mu ne jarin mu
Sannan abinda ke burge ni duniya, kowa nada alkhairin sa ko sharri
To amarya ga angon ki
Nasan kina da tarbiyyar ki
Karki dinga yi mai tsaki
Kisa ya dinga labarin ki
Shima nasan yana kishin ki
Baison abinda zai bata ki
Zai kare dukkanin hakkin ki
Ki dinga mai kalaman baki
Kullum ya kara soyayyar ki
Yau farin ciki ya karu, gun ango naga ba rufewar baki soyayyah
Ahhh soyayyah
Lyrics powered by www.musixmatch.com