Credits
KOMPOSITION UND LIEDTEXT
Adam Asm
Songwriter:in
Lyrics
(ASM record)
(Yane)
Ni da kasuwancina
Bama rabo da juna
Safiya, dare, rana
Na maida hankalina
Bana da lokacin da zan zauna
Da masu gulma
Mai nema a hankali
Samu zai ishe shi
Ba'a yin rashin ruwa
In an tona yashi
Tillas za'a samu karfi
Gun yaro matashi
Wake ko yakanyi 'ya'ya
In an masa feshi
Ashe dauka tana gurin
Masu zubin adashe
Amma wahala kubarta gun
Wanda yake da kyashi
In rabbi yayi ma baiwa
Zai bata ran shi
Mun fito Allah kabamu sa'a
Na sanmako
Gun neman na kai
Sai da nawa bama taku
In dai da nasara ga mai hima
Takayin rako
Kunga kalar sana'ar da mukeyi
Ta ishe mu komai da akeyi
Ci da sha har kayan yayi
Gashi dai asirin mu a boye
Maula bama yi
Godiya ga sarki mabuwayi
Jallah
(ASM record)
(Yane)
Written by: Adam Asm