Lyrics

Ragass
Mage ta makance
An ci bagas
(Prince Production)
Ko dukan mazan jiyan
Haushin masu dan wuyan
Baccin kan gadon kayan ba
Mun zama sha dakan gidan turmi
Sha gwagwarmayan ba
Ba yan bani na iya ba
Ba yanda dan mutum yake yi
Tunda yana gani muke yi
Har wani rangaji suke yi
In muka dan kado na yayi
Ba shiru mukayi ba
(Mage ta makance)
Ragass (eh mana)
An ci bagas (kai don Allah fada masu)
Ragass (eh mana Gwanja, ahha)
An ci bagass
(In tayi ruwa muje mu diba)
(In taki yin ruwa, toh ba rijiya bace ba)
(Masai ce, ahayye)
Mata duniyar ku is accuracy
Da yawa-yawan ku naga intelligency
Kyau ta kafar ku har zuwa presidency
Ya Allah ka bamu governors mata
Rintsa ido before a tauna gauta
Allah ko cikin gari bamu rabo (Ameen)
Allah ko cikin dawa bamu rabo (Allah ameen)
Allah ko cikin dare ko rana (eh mana)
Bai wa makiyan mu nisan kwana
Ko dan muyi tayi suna kallon mu
Suna ta jin haushin mu
Muna ta babban kamu
Ya Allah ka maida taure gwanki (ameen)
So samu a maida mota jirgi
(Ai gwara ta tashi tayi ta lulawa)
(Tayi ta yin saman, tai sama, tai saman
(Ta dawo in lokacin zuwan ya kawo)
(Hayyah, eh mana)
(Eh mana)
(Eh mana)
Ragass (eh mana, hayya)
An ci bagass (eh mana Gwanja, ahha)
Kin ji irin kidan ki tasa
Daga tasa salon siyasa
Tantabarun Sani sanga-sanga
Kaza mai kike da kwan ki?
A gidan kwai
Aka dafa kwai
Aka ba kwai
Tallan kwai
Ya sai da kwai
Ya siyo kwai
Yadda dillin
Takan yi dillin
Haka dillin ma
Ya kanyi dillin
Yadda kaza
Takan yi kwan nan
Haka kwan nan
Ya kan yi kaza, ah-ah
Ragass (eh mana)
An ci bagas (kai don Allah fada masu, kai)
Ragass (eh mana Gwanja, ahha)
An ci bagass
Ragass (eh mana)
An ci bagass
(It's Prince on the mix)
Written by: Ado Gwanja
instagramSharePathic_arrow_out