Credits
AUSFÜHRENDE KÜNSTLER:INNEN
Ali Jita
Künstler:in
KOMPOSITION UND LIEDTEXT
Ali Jita
Songwriter:in
Lyrics
[Verse 1]
Toh, mafarkina
Ke nake gani dare rana
Kada ki raunanan tunanina
Ki garzayo gare ni ʼyan mata
Idanuna, ba su iya jure kukana
A kan jiran ki zuciya ƙuna
Me ya sa kike gudu na ne?
[Verse 2]
So ruwan zuma ne
Amma ku san kala-kala ne
Mai armashi wanda babu wahala ne
Ku ce da kishiyan ɗayan ruwan maɗaci
[Chorus]
Rayuwa, rashin masoyi damuwa
Kamar a rayu ba ruwa
To me ake da rayuwa in babu so?
Rayuwa, rashin masoyi damuwa
Kamar a rayu ba ruwa
To me ake da rayuwa in babu so?
[Verse 3]
Wallahi ke na bai wa yardata
Ke za ni karkaɗawa jitata
Masoyiya ke nake fata
Na samu tabbacin mafarkina
Ina da tambaya
Ki ɗan tsaya
A duniya, shin za ki rayu in babu so?
[Chorus]
Rayuwa, rashin masoyi damuwa
Kamar a rayu ba ruwa
To me ake da rayuwa in babu so?
Rayuwa, rashin masoyi damuwa
Kamar a rayu ba ruwa
To me ake da rayuwa in babu so?
[Verse 4]
Ke nake gani, kin yi sansani
Ke nake tunani
Na ji na gani, mai farin jini
Mai kyawun kamanni
Kar da ki ƙi ni sahibata
Ko ki guje ni gimbiyata
Guna daban kike a mata, masoyiya
[Outro]
S-sultan with the beat baby
Written by: Ali Isah Jita