Top Songs By Moussa Yaro
Credits
KOMPOSITION UND LIEDTEXT
Moussa BOUBE HAROUNA
Songwriter:in
Lyrics
Wata rana da safe na shirya zani wuce gona (zanje gona)
Na gano wata yarinya mai kyau a ta dama na (ta dama na)
Har taso ta bugeni da mota ina a keke na (a keke na)
Na fadi ruwan kan hanya na bata kaya na (kaya na)
Ta fito tanata masifa so na shige kewa (shige kewa)
Kauna nata ya kamani gashi tanata min tsawa
Kokari na in nuna mata so (nuna mata so)
Gani dan talakawa ba wanga soso (waga soso)
Amma karambanin talaka sai da na furta
Nace mata, "Son ki ya kamani na gigita"
Ki tallafi dan bawan Allah so ki aminta
Tai mini kallon bisa har kasa tace kaja baya
Watan, wata rana munka hadu bayan na shiga birni
Wankan girma ce na buga sanya ido da ma'auni
Na shiga super market ne nan a cikinsa ta ganni
Nazo zan fita sai ta buge mini kaya na (kaya na)
Tace mini, "Sorry dama tana ta nema na" (nema na)
Ta ban hakuri ta fada mini tanata kewa na (kewa na)
Tun a sanda na barta tace ta kamu da kauna na (kauna na)
Nace mata, "Wayyo baby kin makara nemi wani na
Na riga na samo wata yarinyar an sa mana rana"
Na bata kati na bikin mu a nan mukayo bankwana
Mai wulakanci ya ka ko ka dare rana
So mai kaunarka koda yana a gidan zana (a gidan zana)
Wata rana sai ya zamo hamshaki
Ya zamo gwamna koko basarake
Zance na nakunne Jabir mkyb na fada
Written by: Moussa BOUBE HAROUNA