Lyrics

Nayi dace dake
A sona da kauna
Nace, "Nayi dace dake baby"
Nima nayi dace da kai hubbi
A sona da kauna hakane
Sanka duk ya cike gun rabe
Duba nace miki duba
Nawa kaine kwal tilo
Angona, nayi ma lale
Ka dawo, zan ma fifita
Burina, shine samun ka
Madubina, so yasani nagarta
Ban gani ban ji, indai akanka ne duba
Na fada yanzu
So ni zan wa bauta
So ni zan wa bauta
Ni na shirya, so ni zan wa bauta
Eh ni naji duka kalamanki
Yan mata, ni kece burina
Eh dare da rana ina sanki
Manufata ki zamto mata guna
Ni nai babban dace
Da samunki don kece nasara ta
Na duba
Taka ni kadai tabbas
Ba'a ma murdiya
Komai kace in yi ma masoyi
Ka tabbatar zan iya
So da kauna akwai dalili
Bana gudun tafiya
Duk inda zanje, bazana share ka ba
Jinin jikina yana gudana
Baza'a raba mu ba
Alkawar ni dakai mu dauka
Bazamu karya shi ba
Kuma dankon sanka ni na dauka
Bazana aje shi
Zanyi yaki da makiyanka
Bazana kyale su ba
Yan mata aha-aha yan mata
Yan mata ihe-ihe yan mata
Nagano lalai so yayai mun gata
Da naganki mu zauna tare nake fata
Kashi tsoka jini na saman sa kice fata
Idan bake ba toh ni sai dai makabarta
Mu rayu a tare kalman so nai miki bita
Abar sona cikin raina tini kin kwanta
Idan dai kina a gefena ban tina Binta
Wayyo ni
Dadi yasa na rikice
Hubbina yi min wake karda na zauce
Kalaman so in bana naka ba na mance
Written by: Moussa BOUBE HAROUNA
instagramSharePathic_arrow_out