Lyrics

(Maiatamfa on the beat) Matsayin ka baya canzuwa Tunda a son ka na gama kamuwa Kaine ka kore mini kishin ruwa Kuma kai ka cire ni a damuwa Ah yeah, baby ki daina fadin haka kin ji Zan fada kowa sai ya ji Zafin so ya wuce yaji A'ah ban fama maka kurji Kinga dai na shaku dake Soyayyah ce Rike amana karki sake Zan alkince Na zo da al'bishir kace goro Na tara baituka cikin daro Gani gaban ki zanyi sauraro A gidan mu ance ka turo Farin ciki ba zaya misaltu ba, kika zamto mata ta Mun zarce Laila da Majnoon, banso kayi min rata Kalaman ki da sanyi dan matso ki gyara mini hula ta Komai ka sani dole zanyi maka don samun Aljanna ta Soyayyah ce Son ki a raina bazai fice ba Nina sani ko ban fadi ba Ba wacca zata zo ta maye gurbin ki Kiyi dashen so har yayi huda Don haka dole tsiron zaiyi tsada Kin gama naki ni za na zubo taki Zanyo fada da wanda ta kalle ka Domin ina kishin ka Burina daya a kaini gidan ka Matsayin matar ka Na matsu Nima na matsu Inga kin shiga lalle Zan banu Nima zan banu Aka raba ni da kai Sahiba (bi) ni da ke (kai) soyayyah ce
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out