Similar Songs
Credits
KOMPOSITION UND LIEDTEXT
Auta Waziri
Songwriter:in
Lyrics
[Intro]
Auta Waziri kuke ji malam
(Sultan with the beat baby)
[Chorus]
Na ba ki so ke ma ki ba ni ƙauna
Ki kula da ni sam kar ki ɓata raina
Na ba ka so kai ma ka ba ni ƙauna
Ka kula da ni sam kar ka ɓata raina
Na ba ki so-so-so in ba ki ƙauna
Na ba ki so-so-so in ba ki ƙauna
[Verse 1]
Ke ce guda wacce ki ka sallama min
Na sa a rai ke ce za ki agaza min
Ko faɗuwa zan yi za ki tallafa min
Ɗan zo in gan ki jiki ya ƙara ƙaimin
Masoyiya ke zinariya ce
[Verse 2]
Na ba ka so
Ke ma ki ba ni ƙauna
Ka kula da ni sam kar ka ɓata raina
Na ba ki so
Kai ma ka ba ni kauna
Ki kula da ni sam kar ki ɓata raina
[Verse 3]
Na so ka zo ne ka ɗan tsaya gabana
Tun da na yarda gidanka za na ƙauna
Ka zam mijina jiɓanci lamarina
Jini da hanta kai ne ɓargon jikina
Ina da kai wa zai shiga ƙalbina?
[Verse 4]
Na fara son ki ne bada uzuri ba
In babu ke sai in ji ba za na kai ba
In dai a kaina ne to kin dasa ɗamba
Aya ta farko son ki ba ɗan kaɗan ba
Ke ce guda ki ka zama zaɓina
[Chorus]
Na ba ka so ke ma ka ba ni ƙauna
Ka kula da ni sam kar ka ɓata raina
Na ba ki so kai ma ki ba ni ƙauna
Ka kula da ni sam kar ka ɓata raina
[Verse 5]
Ni kai nake so ƙaryar mai adawa
Ka zam miji guna kai ba ka ɗagawa
Jeka da ƙarfi ni zan ba ka power
Ka fi su ne, kai kyauta halinsu rowa
Kai ne guda wanda rai ke so ƙauna
[Chorus]
Na ba ka so kai ma ka ba ni ƙauna
Ka kula da ni sam kar ka ɓata raina
[Verse 6]
Haka na ji-na ji-na ji ana ta misalai
Wasu na faɗa, wasu ko babu dalilai
Cikin zuciya na kulle ke na ba makullai
Ko da na shiga na ga zinare da tagullai
Don haka a bar mu tare so da ƙauna
[Outro]
Na ba ki so-so-so in ba ki ƙauna
Na ba ki so-so-so in ba ki ƙauna
Oh my God! The Sultan on the beat
Written by: Auta Waziri