Lyrics

Amarya taso zauna a gefen ango
Domin kun dace gare ki ya zam jigo
Ki lallaɓa Mukhtar domin zuma ta fi rago
Auren soyayya da ba a yi wa jayayya
Zainaba amarya, Hamisu ne mai waƙa
Na zo ni gare ki da wata babbar saƙa
Buɗe kunnenki amarya ga wata waƙa
Kin yo aure ne muna ta sa albarka
Da ni da Mudan Auta shi yasa nai waƙa
Amarya ʼyar gidan albarka
Ki zauna
Guɗar da muke za mu yo ta bayan aure
Burinmu ki zauna gidan mijinki ki tare
Zainab Mama amarya ki yi ta fesa turare
Mukhtar chairman da ke da shi a yau an ɗaure
Murna muka zo mu taya ku ranar aure
Amarya, koma jikin mijinki ki zauna
Idan kin yi hakan soyayya ta zama ƙauna
Ranar wanka cibi dole sai an nuna
Salisu Yaro nawa yai rawa don murna
Amarya Zainaba Mama yau ga rana
Mun shaida angonki ba ya gugar zana
Mukhtar ango yanzu ka ɗarar ma gwauro
Ka yo auren so a yanzu ka fasa taro
Ka fi su Ghali Dorayi suna nan a soro
Mudassir Auta na san yana nan a hanya
Ya kusa aure tunda shi yana soyayya
Amarya ga tamburan mai waƙa
Buri na a ce ki tashi ki taka
Ango ka zo ka ɗan albarka
Duka abokanai suna gaisheka
Ismaʼil Barewa ban gangarka
Mamana a yanzu zan gaishe ki
Maman amarya maman ango dole yabonki
Ranar aure, yau ne ake bikin ʼyaʼyanku
Soyayya silar zama na amana
Nan za na tsaya nima gida zan koma
Suna na Hamisu S Yusuf ne
Breaker ni ɗin na ʼyan Ɗorayi ne
Sai wata rana ʼyan uwa na bar ku lafiya
Written by: Hamisu Breaker
instagramSharePathic_arrow_out