Lyrics
Ka taimaka min
Tallafa min
Ka tausaya min
Soyayya ce sila
A kai na wahala
Share min kwalla
Ina cikin duhu
Ka zo da fitila
Taimake ni ka so ni ina bara
Ka cire ni a kangin rayuwa
Na jiyo ki da baki kina fadin
In cire ki a kangin rayuwa
Kai na zaba kai za nayi
Soyayya nake ma tayi
Don Allah kar kace ba kayi
Masoyi tsaya ka tausaya
Soyayya ta dauka
Ka rataya
Kyawun halin ka shine ya tafi dani
Ka taimaka min kayi rayuwa dani
Na kubuta a tarkon masu cutar dani
Sai inyi rayuwa
Daidai da kowa
In samu natsuwa
In kayi kulawa
Taimaka min Allah ya taimaka maka
Ya cire maka dukkan damuwa
Na jiyo ki da baki kina fadin
In cire ki a kangin rayuwa
Naji zancen ki da kika yimin bayani
Bude kunne kiji amsar ki a gare ni
Kin ban soyayya na karba
Hannu biyu nasa na tarba
Nayi miki alkawari bazan guje miki ba
Nayi damara ta nasa danba
Ni kika zaba za muyi hubba
Sani daya a cikin duka lamba
Gani gaba
Indai soyayya ta ce kin samu
Sanya a ran ki za ayi auren mu
In Allah ya yarda za muyi rayuwa
Matsayin ma'aurata za muyi shakuwa
Ba gudu babu ja da baya
Son ki zan tsaya
Zan zauna dake har karshen rayuwa
Lyrics powered by www.musixmatch.com