Similar Songs
Credits
AUSFÜHRENDE KÜNSTLER:INNEN
Umar MB
Künstler:in
KOMPOSITION UND LIEDTEXT
Umar MB
Songwriter:in
Lyrics
Na rike soyayyar ki
Har abada ban yarba
Ya shige ko'ina lamarinmu
Ba wanda baisan zancen ba
Sun sani dukanin dangin mu
Ko suma baza su raba ba
Wanda duk yaji labarin mu
Bazai ki yayai mamaki ba
Karki manta nidin naki ne
Mai chaza launi wai yaso yake ne
Iya sanina ni gwarzon namiji me
Gashi so yaci karfi na ina sane
Zuciya sa mini rauni
Yarda nasoki dan Allah
Ba dan kudi ba ko sura
Yardar ki zamto mini fitila
Banda tsumi banda dabara
Tinda kauna muka kulla
Daure kiyo mini sitira
Sanki ya jawo mini matsala
Kinki yarda mu jera
Daso nake fama
A rai yana girma
Kin saka mini koma
Jiki yana kyarma
Kwayar idanu ma
Kece suke nema
Na aje girma
Kauna nake nema-aa-aa-ah
Da saki so shi mai sanki ke yar yarinya
Da zaki samu dukanin gata duniya
A kanki zana jure dukanin nisan tafiya
In kika kini na kama rashin lafiya
Ruwan hawaye na
Bazai bar zuba ba
Haba rabin raina
Kece nake duba
Kina tinanina
Ko a makwanci
Kin ci mini amana
Kin fasa kirji na
Dama zaki gane zaman duniya
Dama zaki gane rayuwar duniya
Dama zaki gane zaman duniya
Written by: Umar MB