Credits
KOMPOSITION UND LIEDTEXT
abdulkadir tajuddeen
Songwriter:in
Lyrics
AD music studio
C one producer
Umarninki a kai nake mahaifiyata
Kece ta farkona, a duniyata
Umarni
Umarni
Umarnin Mama
Shine a kan gaba
Duka dan kwarai bai kusheki
Kuma baya zaginki
Sai dai yayi gadinki
Mamana Allahu ya samin son ki
Ya sa mini kaunarki
Gareni ba wata tamkar ki
Mamana (mama)
Ke kika cece rai na
Kika bani suna
Kika sa ni jerin 'yayanki (Mama)
Na ginu kan tarbiyarki
Bana saba umarninki
Komai kika ce hakanan za'ai tunda kece-kece (mama)
Masoyiyata ta duniya
Har ma da lahira
Umarninki nai a gaba bazan daina biyayya ba
Mama
Mama
Batabarinai kuka masoyiya Mama
Farincikin dake duniya kece kadai Mama
Sarauniya, matar Baba
Girmanki ne Ummah
Ko ba abinci
Ko ba ruwan sha bakya kin zama Mama
Ki rayu cikin talauci da arziki Mama
Kin sha wuya, a duniya wayyo ni Mamana (masoyiya)
Ba'a fiki komai ba (ina nan tare dake mamana)
Mama ba'a kaiki komai ba
Umarninki ne, a kai nake, bazani sauko ba
Lyrics powered by www.musixmatch.com