Lyrics

Anyi aure, ga ango ga amarya soyayya
Amarya, ga ango ga amarya
Soyayya, soyayyayaaah
Soyayya ruwan zuma ce
Musamman in kunyi dace
Da juna a takaice
Sai ku zam da farin ciki
Baku babu bakin ciki
Tinda kunyi aure da juna
Sai kuyo zaman amana
Har abada ku zauna
Tafiya har gidan aljana
Anyi aure, ga ango ga amarya soyayya
Amarya, ga ango ga amarya
Soyayya
Anyi aure, ga ango ga amarya soyayya
Amarya, ga ango ga amarya
Soyayya
Yau ga amarya ga angonta
Ba abinda ke damunta
Sai farin ciki fuskarta ku duba
A yau ta cike dukan burinta
An bata zabin ranta
Sarauniya take jin kanta na duba
A hankali rawar taka
Amarya, yau bakida doka
Bude idonki farka, ba bacci kike ba
Ba mafarki kike ba
Mijinkine, tinda an daura
Angonki ne, shaidu an tara
Ni kuma wakarki na rera miki amarya
Anyi aure, ga ango ga amarya soyayya
Amarya, ga ango ga amarya
Soyayya
Babu rabuwa dake dashi
Hakori da dasashi
Ke nama, shi ko kashi
Taraiyar guri daya
Yau gashi an daura muku
Dangi sunata yaba muku
Rayuwa ta chanja muku
Karku yarda a bata muku
Fahimci ku kula
So da kauna shine silla
Ki mai abinci kala kala
Kisa shi yayai murna
Anyi aure, ga ango ga amarya soyayya
Amarya, ga ango ga amarya
Wanan amarya da kyau take
Sai walwali ango yake
Kai har kaman-ni masuke
Kowa mamaki yake
M Shareef shaida nake, shaida nake
M Shareef shaida nake
Ga waina ga wuri
Yiriri-ayiri
Masu kawo hari
Nan gani nan bari
Rabuwa sai mutuwa
Wanda ke jin haushi ya daina
Rabbi ne ya nufa zaku zauna
Da'iman abadan zaku zauna
Daga nan duniya har aljana
Ya Allah ka amsa
Ya Allah ka amsa
Written by: Umar M Shareef
instagramSharePathic_arrow_out