Similar Songs
Credits
KOMPOSITION UND LIEDTEXT
Tasiu TK
Songwriter:in
Lyrics
Idan babu ke babu ni rayuwata
Ke kadai nake kira da kaddara ta
Idan babu kai babu ni rayuwata
Kai kadai nake kira da kaddara ta
Idan ance zo mu zauna mu rayu tare
Dole sai da zo mu saba
Duk inda kaji anyi buda akwai amare
Dole kwalliya a caba
Kalaman da su sa masoyiya hawaye
Zatazo a so ta saba
Naji na gani a so zamu rayu tare
Tunda ni dake na saba kaddarata
Ka taso gareni zo taho mu dauki hoto
Tunda dai an baka ni
Kawaye suna fadin hakan kawai na matsu
Duk su barmu ni dakai
A raina da zuci kai nake yin ambato
Kar da kayi nisa dani
Zani bika ko ina zamu tare
Tunda ni daki na saba kaddarata
Kin san babu wanda zaya kaiki a gurina
Sonki ni na fara
Sannan duk ilahirin samarin a ganina
Na ishe su kar su fara
Ace ko guda da zaya biki a sanina
Baki sauraron batunsa
Na riga da sani zuciya tana so
Ke nake gani a littafin kaddarata
Inama ace abani dama ko da wasa
Ni kadai na malleke ka
Ace duk abinda rai da ruhi suka kunsa
Zani bayyanar gareka
Da kamshinka zani gane kaine ko ba ido ba
Na riga da na waye ka
Da anga naci kwalliya na sa turare
Ba abinda za'ace sai wajenka zani
Idan babu kai babu ni rayuwata
Kai kadai nake kira da kaddara ta
Written by: Tasiu TK