Lyrics

Rayuwa zatayi kyau ni dake, rikicin aure bama ciki Mu kasance tare a ko yaushe, ni dake ba mai yin gardama Rayuwa zatayi kyau ni dakai, rikicin aure bama ciki Mu kasance tare a ko yaushe, ni dakai ba mai yin gardama Soyayya ba'a karatu, in ka iya tana kanka Komai zakayi, yi shawara yafi kayi gaban kanka Gunki na doso da tambura, nafiso ki tattaka Ban so kibani tazara, in kika yi zan hauka Wasa kala kala, zamuyo dake duka Nasaba bada zuciya, a yanzu kema ga taki Oohh Sarkin yaki, a sannu-sannu so ya girma Nice mai girki, kai kuma ka wuce gun nema Abincin girma, kaci tuwo miyar ga nama Naji dadi-dadi, kace nice ta hannun dama Nisan kwana Allahu yayi ma Dadin kallo kazarce korama, hakane Kin iya satar zuciya (oho-oho-oho) Zani kiraki guda holiya (oho-oho-oho) 'Yanmata kin masu bulaliya Kece dai burin duniya Nai babban kamu nan masoyiya Zani baki kaina, in saki a jiki Shi mummuna bashi kwalliya (koyayi sai an gane) Kyawun kallo na gamai ado, komai kai dai-dai ne Mace batayi in ba salo, koko nai karyane Saurayi kai ne na tsayar gwani, kowa ya kasa kunne Mata in bamu ba gida (haka ne) Matsayinka daban ne (daban ne) Oooh Rayuwa zatayi kyau ni dake, rikicin aure bama ciki Mu kasance tare a ko yaushe, ni dakai ba mai yin gardama
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out