Top Songs By Kasheepu Amjad
Similar Songs
Credits
KOMPOSITION UND LIEDTEXT
kashiful suleiman tajir
Songwriter:in
Lyrics
Kida
M sharrafi
Mmmm zanen zabo, so ya taru kwando kwando
Yayai mana riga, sanan kuma yayai mana wando
Okay
Kasheepun kida
Mmm zanen zabo, so ya taru kwando kwando
Yayai min riga, sanan kuma yayai min wando
Fara'ar fuskarki ki min mana indo indo
Na zamo zabin ki
Ki fadan amsar ki
Da kalaman baki
Na shigo tarkon ki
Ni kaunarki nakeyi ki duba kigani
So ya mamaye ruhi ya kwanta a jini
Ina sanki nidai rabi na jikina
A dakin gida nake so ki kwana
Wuya ko da dadi, kina nan a raina
Ina amsa suna kece mahadina
Taho madadina
Kizam mallaki na
Ke dai zanyi jira so yayai mana zanen zabo
Muyai tafiyar nasara mu bar kula mai yin zambo
Sanda ruwa na hawaye zaya zubo kiyi tarbo
Zo ki ririta ta zuciya kar tai gembo
Bakina ya fadi dake nafi so muyi sabo
Zanen zabo, so yayai mana zanen zabo
Nazo gunki
Domin kauna
Zan kai miki
Ki sani so zanen zabo ne
Bai chanja ba
Ki sani so zanen zabo ne
Da bai chanja ba
Ki sani so zanen zabo ne
Da bai chanja ba
Bai chanja ba, to ai bazai chanja ba
Ba'a furta kallamar soyayya da wasa
Daga ji kunsan ina na dosa
Kanki bani faduwa fili na gasa
Zan bada kaina
In saida raina
Tunda kin yarda nine zabinki, bazan saka ki kuka bah
Komai kikayi domin soyayyace, bazai sakani haushi bah
Bazana juya ba, bazanyi koh budurwa bah
Bazana sauya hali ba, bazana kara aure bah
Na sameki me kuma yayai saura ah
Kawa abokiyar hira ah
Ki bani zuma ungo madara ah
In nayi murna, kece silana
Nakai karshe a sanki can kololuwa
Sanki a raina ya zama zanen zabuwa
Kece farin ciki nah
Kumah kece bakin ciki nah
Samu na lafiya naaa, ace ke kike kirana
Tunani nake in ba ke, ina zana sanya raina
Dan kece kike shigar mini har kuryar zuciya ki zauna
Banso a sanki in makaro
Kauna ki bani yafi aro
Muryanki zanta saurari idan zantukan kike
Na baki duk amana
Saman guri in zauna
Amma zuciyarki nake buri dan zaman lumana
Yar yarinya nazoo miki
Soyayya ta, nakawo miki
Idan kin amsa, na gode miki
Sai kin soni zan samu damar nuna farin ciki
Zanen zabo na gaya miki bai goge ba
Zanen zabo na san bazai goge ba
Zanen zabo ke kin san bazai goge ba
Zanen zabo na gaya miki bai goge ba
Ina nayi murna kece silana
Na kai ƙarshe a sanki can kololuwa
Sanki a raina ya zama zanen zabuwa
Ke dai zanyi jira so yayai mana zanen zabo
Muyai tafiyar nasara mu bar kula mai yin zambo
Sanda ruwa na hawaye zaya zubo kiyai tarbo
Zo ki ririta ta zuciya kar tai gembo
Ba'a furta kallaman soyayya da wasa, yarinya nazoo miki
Soyayya ta, (beat amjad record) nakawo miki
Sai kin soni zan samu damar nuna farin cikiiiii (midget mix)
Lyrics powered by www.musixmatch.com