Similar Songs
Credits
KOMPOSITION UND LIEDTEXT
umar musa sulaiman
Songwriter:in
Lyrics
Kin bani so da kauna masoyiya kin fitar dani a kunci
Tunda ka isar da sakon zuciyar ka
Zancen ka ke saka ni bacci
Ke mai yin ado da jan baki kalamanki na ta yawo a raina
Kinga na raini zuciyar da kaunarki
Karki ja da baya bar guduna
Kinga zan jure in yi tataki zafin rana zan jure jikina
Sarauniya sannunki ina ta gaisuwa sannunki zinare
Zo ka bani hankalinka
Dauke ni je ka saka cikin 'yan uwanka
Zan so na zama ahalinka
Na zauna dawamar farin cikin ka
Dangina sun lamunce na bika
Dadi wuya sun ce, "Min kar nabar ka"
Na yaba halinka
Haiba da dukka natsuwar ka
Sannunka
Saka ni a ranki
Uwar gidana kan daki
Sun ce, "Na haukace domin ki"
Rashin sani na san da nake miki
Muna koyan so ne da soyayya
Kin soni tun kafin ni in shirya
Kun ganta soyayyar ta shiga zuciya mai kyali ya zinare
Teku bai ki amai da di ba
Kara mini soyayyaar ita na zaba
Ina son ka banyi kure ba
Ai babu laifi kyautar dana karba
Bani ba kuka don bazai mini kyau ba
Nisanta zam kusanta mu duba
Na yaba halinka
Haiba da dukka natsuwar ka
Sannunka
Written by: umar musa sulaiman