Lyrics

Ko ana dara a hidda uwa Damuwar ki takan jawo damuwa Kukan ki yakan janyo tabuwa Shagwabar ki tana sani dimuwa Ganin ki yakan sa nayi kaguwa Bana zama inda ake rabuwa Ni nafison masoyin dake rayuwa Ko sun fada a take zasu shirya Dauki littafi Rubuta sunan ka A kasa suna na Shine shaidar za muyi rayuwa Dauki littafi Rubuta sunan ki A kasa suna na Shi zaya zam shidar rayuwa Ga littafi na Shi ya zama aboki na Ko a cikin daki na Ko a gurin kawaye na Cikin sa kwai so har kauna Zai gyara yau har da gobe na Da maganin matsaloli na Ya canja rayuwa ta Kina kama da dangi na Zubin ki sak na kanwa na Yar doguwa abar so na Za kiyi kyau da yin murna Ni burina in burge ki Ki mance damuwar dake ran ki In zama nine komai naki Samu guri ki zaunawa Nagode Allah da ya cika burin Ya maida komai a tsarin Yanzu babu mai mini gorin Ya bani tari-tarin Soyayya gata gaba na Ka canza tsarin kai na Harma jina da gani na Komai da komai ka saita
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out