Featured In

Credits

KOMPOSITION UND LIEDTEXT
abdulkadir tajuddeen
abdulkadir tajuddeen
Songwriter:in

Lyrics

Soyayya dabarar zuciya
Idan da ke zan huta da rayuwa
Soyayya dabarar zuciya
Idan da kai zan huta da rayuwa
Kin mini bazata
Nayi mamaki ashe so na kin gasgata
Ooh na fada kogi sabo
Nasan cewa ruwan ciki zan debo
Wannan ruwan akwai kada ciki
Soyayya ta tayi fika-fiki
Nasan ka ganshi zakayi mamaki
Har a rai shi nake so ooh
Shi ne yasa zuciya ta ta makance
Sabuwar duniyata ke ce
Mai kore damuwa ta kece
Tunda na ganki hankalina ya kauce
Ai dagani ko ba tambaya mun dace
Hankali ya yi daban da idon gani
Zuciyar da kake bina da magani
Soyayyar wani ce ke san sani
Shi kadai nake so amma bai gani
Cuta take shirin kamani
Domin nagane baya so ya kulani
Ahh
Soyayya dabarar zuciya
Idan da ke zan huta da rayuwa
Soyayya dabarar zuciya
Idan da kai zan huta da rayuwa
Written by: abdulkadir tajuddeen
instagramSharePathic_arrow_out