Top Songs By Nura M. Inuwa
Similar Songs
Lyrics
Rana taiman zafi inuwa tayo 'kuna a gurina
Ina zansa kaina soyayya asali na
A cikin ku wazan 'dauka aa ah
Eh rana da zafi Inuwa da 'kuna cikin ku waye zani 'dauka
Soyayyar su tazammani tsani
Um Rana zafi inuwa 'kuna wai a ina Yakamata ki zauna
Wannan babban al'amari ne
Rana da zafi inuwa 'kuna
Sauri akeyi ba gu na zuwa
Taura biyu baki zai tauna
Cikin ku ni wazan 'dauka waza na 'kyale so ra'ayi na
Kowadanasa abinda yazoman ni zuciya 'daya ce a gurina
Ni na sakan-kance a cikin rai tun Fil-azal nafidda gwani na
Kunsa 'kwa'kwalwata zauce hankali ya 'dauke gani na
Rana da zafi inuwa 'kuna
Sauri akeyi ba gu na zuwa
Taura biyu baki zai tauna
Ke hankali tsaida shi wuri 'dai kinsani nike 'kaunarki
Dake nasabawa soyayya kina kirana da mallakin ki
Farinciki shi nake yawan yi kowace rana idan na ganki
Gujewa duk matsalar soyayya kisani ranki abar fahari na
Rana da zafi inuwa 'kuna
Sauri akeyi ba gu na zuwa
Taura biyu baki zai tauna
Eh mazaya sa ki 'dakko bare da hannuwanki ki tura na dangi
Ki 'kara yin nazari da tunani yin haka zai jawo maki zagi
Shi hannu naka baya rubewa ka yankewa ayo zargi
Na yunkuro banyi jinkiri ba soyayya a gareki na nuna
Rana da zafi inuwa 'kuna
Sauri akeyi ba gu na zuwa
Taura biyu baki zai tauna
Rana da zafi inuwa 'kuna
Sauri akeyi ba gu na zuwa
Taura biyu baki zai tauna
In na biyewa ta zuciya ta zanyi abinda ni zai dame ni
Batu akeyi na soyayya duk jama'a dakai suka sanni
Kai kuma gashi na cuso kai dole a raina naita tunani
In ka shigo lamari ya 'baci bana gudun maganar manya na
Rana da zafi inuwa 'kuna
Sauri akeyi ba gu na zuwa
Taura biyu baki zai tauna
Um akanki ni kambu na 'daura ga ajiya ki rike mani tuta
Akala ninna sau maki to duk inda kikeso sai kija ta
So nayi nisa dan Allah ki gane wai yaushe zai saki zuciya ta
Ki damke mai sanki haka shine tino halarci sai 'dan amana
Rana da zafi inuwa 'kuna
Sauri akeyi ba gu na zuwa
Taura biyu baki zai tauna
Eh banyo zato ba babu tsammani zuciya tawa kika sace
'kaunarki yama za'ai na daina soyayya kin san ruwan zuma ce
Abar yabo na abar tunani karda kinyarda akanki na zauce
Farinciki shi zai sameni duk ranar da na ganki gidana
Rana da zafi inuwa 'kuna
Sauri akeyi ba gu na zuwa
Taura biyu baki zai tauna
Eh rana da zafi Inuwa da 'kuna cikin ku waye zani 'dauka
Soyayyar su tazammani tsani
Um Rana zafi inuwa 'kuna wai a ina Yakamata ki zauna
Wannan babban al'amari ne
Rana da zafi inuwa 'kuna
Sauri akeyi ba gu na zuwa
Taura biyu baki zai tauna
Written by: