Lyrics

[Intro]
Mai sona zama ginshiƙi na zamto danga
Amince mini sai nace da ke son barka
Zuciya ta kwan da binciken ʼyar baiwa
Ashe ke ce kika zam cikon numfashi
[Verse 1]
Mai sona ka zamma ginshiƙi ni danga
Amince mini sai na ce da kai son barka
Zuciya ta kwana binciken ɗan baiwa
Ashe kai ne za ka zam cikon numfashi
[Verse 2]
Eh! Faruwar so ne abin kamar a mafarki
Bayyana shi gare ki ne ya zam jan aiki
Za na kare hakinki ba ni son ki yi raki
Ban ruwan ƙauna da za na sa a maƙoshi
[Verse 3]
Na riga na fara sonka tun ran farko
Adanawa nai a zuciya tai dako
Aka ce giji lahira a dole na sauko
Tunda dai na gane kai ka min rarrashi
[Verse 4]
Gun ki zan yi ginin gidan Zago mai ƙwari
Zan yi ƙofofin shigar shi tari-tari
Ba ni son a rako ni gun ki jin labari
Tunda dai sirrinmu namu ne ɓoye shi
[Verse 5]
Zuciya sai babu kai ta kan san ƙunci
Ba ni son rabuwarmu ko gurin yin bacci
Ka yi mun komai a sonka ban jin ɗaci
So nake kullum na gan ka ban son fashi
[Verse 6]
Duk yabon da na yo gare ki ce nai daidai
Zo mu zauna ba ni son ki min nisa dai
Ambatawa nai kisa a rai ni ne dai
Naki ɗin nan kin zamo bugun numfashi
[Verse 7]
Ni a kan ƙaunarka ba ni neman sauƙi
Dan akan ka ina shirin faɗa da Sayaki
Ko a bacci nawa kai nake wa mafarki
Mai shirin wara mu yai abun ban haushi
[Verse 8]
Kin gani dai ke kaɗai kike min ƙamshi
Kin riƙe ni da gaske ba ki son garwashi
Tunda dai a kwararafa ake jin danshi
Za na zauna gunki sonki babu irin shi
[Verse 9]
Mai sona ka zamma ginshiƙi ni danga
Amince mini sai na ce da kai son barka
Zuciya ta kwana binciken ɗan baiwa
Ashe kai ne za ka zam cikon numfashi
[Verse 10]
Mai sona zama ginshiƙi na zamto danga
Amince mini sai nace da ke son barka
Zuciya ta kwan da binciken ʼyar baiwa
Ashe ke ce kika zam cikon numfashi
[Outro]
Ashe kai ne za ka zam cikon numfashi
Ashe ke ce kika zam cikon numfashi
Ashe kai ne za ka zam cikon numfashi
Ashe ke ce kika zam cikon numfashi
Written by: Hamisu Breaker
instagramSharePathic_arrow_out