Top Songs By Nura M. Inuwa
Similar Songs
Lyrics
Ehhh-hh-hh naja sun ja sun gudu
Dan na zamto ki gudu
Mai far mani bai cin mani nazam garnakaki
Yau gasa ake kan Hindu
Idan na saba nai kudu
Wanda yayai shirin hanani lalai zaiji jiki
Ni uban maza ja yaki
Mai shiga da kayan tsaki
Yara bushiya waje yakai nata yi ciki
Ka gagari kamu bardi
Saiwar kasa ko mai dagi
Inya takura wa kai haka zayayi haki
Fargabar ga mugun dutse
Wanda ya daka yayai tsartse
Mai tsoron fada bashi iyawa da bakaki
Ga ruwa a hanyar daji
Kar ku doshi gefen burji
Tunda naji shika ba'a yi sai da masaki
Ni tsumagiyar kan hanya
Sanya yan maza suyi jinya
Duk wuya dage na jure duka da madaki
Kai da kaji ihun zaki
Namun dawa zasuyi raki
Shi ko damusa an tabbatarwa sabo yake
Na zamo katangar karfe
In an gwara kai a dafe
Ga tsinin kaya jiki a soke yayi baki
Ni buhu na borkono ne
Idon makiya na tsole
Tankade ni ba'a yi a fai-fai kamar tsaki
Gulbi ya ciko ya batse
Dole rayuwa ta datse
Wanda duk ya tsallake shi toh yayi arziki
Kaifi a taba a yanke
Tsumi za'a sha a warke
Shuka ta gari bata yabanya cikin haki
Tsamiya mazauna iska
Ku kirani kokon kuka
Wanda ya shigo gareni zai zama mallaki
Kunga in na tako sa'a
Nai fice gurin mai ba'a
Hindu zata zam tawa koda da farmaki
Ni ba gwani ba kan soyayya
Amma dani ba'a jayaya
Wanda duk yayo to zaiyi kwanan bakin ciki
Kanbu na mutsuka gaba shi
Sai kaga yan maza sun tashi
Wanda yayi kas da kansa shi zai farin ciki
Fatana na samun Hindu
Na rike ta mu hau kan tudu
Wanda duk ya tsammace ni shi keda alhaki
Ko ku soni ko ku kini
An buga dani an bar ni
Kanta Hindu zana cimma kowa daki-daki
Lyrics powered by www.musixmatch.com