Lyrics

Bamu labari Bamu labari Bamu labari Bamu labari Sai hakuri zaman duniya Zaman duniya Sai hakuri zaman duniya Zaman duniya Ita rayuwar duniya Komai ya kan kare Ita rayuwar duniya Arziki ya kan kare Mulki, sarauta dukka wataran akan share Kai dai rike Allah Shi kadai ya kan hore Ka tsaya akan gaskiya In kayi haka ka more Jiki da jini malam Watarana a sare In ka tuno rayuwar baya Da ta yanzu kaga ta sauya Lokacin kana yaro Kai ta gudu a kan hanya Shekaru da sun shude Sai ka zam tamkar mai jinya Baka gudu baka tafiya Dan tsufa sai an goya Mai kenan zaman duniya? Mai kenan zaman duniya? Ba komai cikin duniya Ba komai cikin duniya Bamu labari Bamu labari Bamu labari Bamu labari Komai ya kan kare ammah banda ikon Allah Kaga mutum a kan mulki Tamkar a mai sallah Sama da goma na gadin su Suna duka da bulala Al'umma suna wahala Shi koh yana cikin daula Dubu sun kwan cikin yunwa Shi koh, koh a jikin sa koh ya kulla Basu damu ba sun rike Allah Burin su ina zasu filla Ammah anbi an toshe kofofi ba gurin kwana Duk tsarin da zasu kawo Su kadai zasu amfana Sun mance akwai mutuwa Zata zo a dare ko rana Zata zo a kan kai na Zata zo a kan kai na Zata zo gidan gwamna Shugaban kasa sai ka tuna Umhum-hum-hum Ya za kai da al'umma? Bamu labari Bamu labari Bamu labari Bamu labari Makaranta duniya Mun zo jarabawa zamuyi Wasu na sa ajin farko Wasu karshe karatu zamuyi Kar mu yarda mu zam a baya Kara dagewa duk zamuyi Muyi abinda akan samu Wanda akayi hani ko karni Mu ci ado muna taku Karshen rayuwar mu ko rami Gida motocin mu Dukiyar mu barin su duk zamu yi Indai akwai wannan Mai za muyo da son duniya? Wayyo duniya Rayuwar cikin duniya Mu bita sannu-sannu duniya Ba madawwama ba ce duniya Roko nake Allah Sa na barta lafiya Cire mini son duniya Budurwar wawa duniya Wayyo duniya Duniya
Lyrics powered by www.musixmatch.com
instagramSharePathic_arrow_out