Featured In

Credits

AUSFÜHRENDE KÜNSTLER:INNEN
Tasi'u Unguwa Uku
Tasi'u Unguwa Uku
Künstler:in
KOMPOSITION UND LIEDTEXT
RR
RR
Songwriter:in

Lyrics

Kin gani na yarda dake azaman mu soyayya matuka
Zuciya ta shaku dake kaunarki ba zan daina ba
Kin gani na yarda dake na so ku ba dan komai ba
Na gujewa zigar jama'a na biki ba dan sun so ba
Ya kike nemaki mini hakin da ban miki farko ba
Kar ki manta halacci na
Abinda nai ki ki dubawa
Tausayinki nake kullum a zuciya duk rana
Bani jin dadin komai abinda ke damun raina
Karda mu rabu da juna wa zai rike ki watarana
Maida kanki diya tagari gareni kar ki cutarwa
Da akwai wani abinci wanda labari ki cida ni
In ka san amsar ka fadan na baka horon gardi
So idan kaji labarin yafi kayishi kabar kauli
In kau kace ba haka ba, da sannu zakayi ganewa
Na ki bin kowace diya na biki dan kiyi mani rana
Sai kawai kika mance hakan ki kai ta sa raina kuna
Tagumi da yawan nazari akanki shi ne aiki na
Tunda kin rikita lamura na hanyar fita ban gane ba
Da ace na san haka so yake bazan sa kaina ba
Anka min kofa ta rago na shiga bada sanina ba
Sai da nayi nisa sannan na gane ban san komai ba
Gaskiya so illa ne sai dai idan kai dacewa
Kin gani na yarda dake azaman mu soyayya matuka
Zuciya ta shaku dake kaunarki ba zan daina ba
Written by: RR
instagramSharePathic_arrow_out