Credits
AUSFÜHRENDE KÜNSTLER:INNEN
Tasi'u Unguwa Uku
Künstler:in
KOMPOSITION UND LIEDTEXT
RR
Songwriter:in
Lyrics
So sanadi zuciyata taji jiki
Tausaya ki mini rana tun da sonki yana raina
So sanadi zuciyata taji jiki
Tausaya ka mini rana tun da sonka yana raina
Zuciya najin tsoron halinku mata bawai ba (so sanadi)
Kar naje na sake ki kaini insa bazan iya tsira ba (so sanadi)
Sai rashin ladabi da rashin da'a duka bazan iya jura ba (so sanadi)
Ina sonki bazan bari zuciya ta makance ba
Rarrafe shine in har kai niyar tashi idan har kai tuba
Kai kasa raina ya dandano dadin soyayya ba wai ba (so sanadi)
Duk abinda kaso zan so shi ko da raina bai so ba (so sanadi)
Toh ka min uziri laifi idan nayi ma kai duba
Na aminta dake da gaskiya ba za kiyi cuta ba (so sanadi)
Asannu ake bi a rayuwa ba wai da garaje ba (so sanadi)
Toh dagaske nake kaunarki ban rike ta mafarki ba (so sanadi)
Son ki shi na rika wallahi ban dauke shi da wasa ba
Na zamo tamkar makauniya banji da gani kaji (so sanadi)
Nai daban a cikin mata ka sanya raina yayi fari (so sanadi)
Tausaya mini kaima kasan yarda son ka yake kaji (so sanadi)
Nayi alkawari zama dakai baza nayi cuta ba
Ni da kai mun zo kama shin ko baka gano ba
Nayi shirin zama matarka na san wasu basa so ba
Tunda Rabbi yaso mun dace dan Adam kuma bai kai ba
Nai dashe na gari na san halin tsiya ban girba ba
So sanadi zuciyata taji jiki
Tausaya ka mini rana tun da sonka yana raina
So sanadi zuciyata taji jiki
Tausaya ki mini rana tun da sonki yana raina
Written by: RR