Featured In

Credits

AUSFÜHRENDE KÜNSTLER:INNEN
Tasi'u Unguwa Uku
Tasi'u Unguwa Uku
Künstler:in
KOMPOSITION UND LIEDTEXT
RR
RR
Songwriter:in

Lyrics

Kece ra'ayi na nima naki nake to yarda dani
Na baki amana ta soyayyar ki nazo nema
To ni bana ra'ayi nemi kalarka kabar fama
Kaine ra'ayi na nima taka nakeso yarda dani
Na baka amana ta soyayyar ka nake nema
Ra'ayi riga ne nakinnasa saurari kalami na
Na kwana in sanki na kuma tashi cikin 'kauna
Bandamu ba komi zakiyi nidai burina
A gareni kizam mata zanso na ganki 'dakina
Eh fatan da kakeyi shine in zama mata gunka
Saidai da rashin dace kazo dan ni bana sanka
Ni bana Sallah kai kanayi jeka mijin sanka
Shine mafita gunka amma so bana ra'ayi
Eh Kece ra'ayi na nima naki nake to yarda dani
To ni bana ra'ayi nemi kalarka kabar fama
Na nuna ina sonki ke kuma bakya man kara
Dan nace zan warke sai naji kaina zan 'kwara
Na damu dake matuka kema nasan kin lura
Gajiya na damu na a zuci taho kiman tausa
Daina bin ra'ayin ruhinka
Je ka nemo jinsin ka
Kece ra'ayi na nima naki nake to yarda dani
Na baki amana ta soyayyar ki nake nema
To ni bana ra'ayi nemi kalarka kabar fama
Ra'ayi na, Ra'ayi na
Ra'ayi na, Ra'ayi na
Ra'ayi na, Ra'ayi na
Kaine ra'ayi na nima taka nakeso yarda dani
Na baka amana ta soyayyar ka nake nema
A'ah da zaki mani uzuri kibarni da wacce nake nema
'Kaunarka nake nema kai kuma bakaman uzuri
Shin mai na rasa a jikin mata ko baka man uzuri
Mai sanka kasoshi hakika shine kyawun lamari
Zan bika nama hidima soyayyar ka nake marari
A'ah da zaki mani uzuri kibarni da wacce nake nema
Kaine ra'ayi na nima taka nakeso yarda dani
Na baka amana ta soyayyar ka nake nema
A'ah da zaki mani uzuri kibarni da wacce nake nema
Na baka amana ta soyayyar ka nake nema
Eh na riga da na bayar da sona gun wata tun farko
Duk yanda take haka zanso ta ra'ayi na ya dakko
Yau na fada garari kasa a soka nake nema
Da zaka amince ni nasa zanyima hidima
Na yarda da kai matuka, ni kuma santa nake nema tabani
Na damu dakai matuka, aure zamuyi in har zatabi
Na kamu da sonka mai sona kaji tausai na
Kaine ra'ayi na nima taka nakeso yarda dani
Na baka amana ta soyayyar ka nake nema
A'ah da zaki mani uzuri kibarni da wacce nake nema
Na baka amana ta soyayyar ka nake nema
Written by: RR
instagramSharePathic_arrow_out