Lyrics

Me ya faru da juna ne? Naga amarya na kokawa
Kukan dadi ne angonki yanata shash-sharewa

Bismillah ya Allah, (ango da amarya na kukan 'kauna
Taimakanni cikin jimla, (ango da amarya na kukan 'kauna)
Na wake ibadulla (ango da amarya na kukan 'kauna)
Dan aure an 'kulla (ango da amarya na kukan 'kauna)
To amarya bar kuka aure kikayishi shine alfarma
Me ya faru da juna ne? Naga amarya na kokawa
Kukan dadi ne angonki yanata shash-sharewa
Amarya mai kirki (ango da amarya na kukan 'kauna)
Na ganki kin 'dauki (ango da amarya na kukan 'kauna)
Burinki kije 'daki (ango da amarya na kukan 'kauna)
'Dakin aur naki (ango da amarya na kukan 'kauna)
Sunnar manzon Allah a rayata shine alfarma
Me ya faru da juna ne? Naga amarya na kokawa
Kukan dadi ne angonki yanata shash-sharewa
Kaima gani gareka, (ango da amarya na kukan 'kauna)
Amarya matarka, (ango da amarya na kukan 'kauna)
Al-'kawari ka 'dauka, (ango da amarya na kukan 'kauna)
Na faranta wa matarka (ango da amarya na kukan 'kauna)
Indai ka daure aure shine za'a yishi cikin girma
Me ya faru da juna ne? Naga amarya na kokawa
Kukan dadi ne angonta yanata shash-sharewa
Huduba zanwa ango (ango da amarya na kukan 'kauna)
A maza ka zama shaho (ango da amarya na kukan 'kauna)
Wani fannin kuma jigo (ango da amarya na kukan 'kauna)
Na amarya 'dan waigo (ango da amarya na kukan 'kauna)
Shawara ce zan baka riketa amana shine alfarma
Me ya faru da juna ne? Naga amarya na kokawa
Kukan dadi ne angonta yanata shash-sharewa
Daga kinbi miji ki sani (ango da amarya na kukan 'kauna)
To kin wuce duk 'karni (ango da amarya na kukan 'kauna)
Kin tsallake mizani (ango da amarya na kukan 'kauna)
Aljanna kike auni (ango da amarya na kukan 'kauna)
Indai kinbi mijinki Aljanna zaki shigeta cikin girma
Me ya faru da juna ne? Naga amarya na kokawa
Kukan dadi ne angonta yanata shash-sharewa
Ga iyayen angonta nan (ango da amarya na kukan 'kauna)
Kuma na gaisheku (ango da amarya na kukan 'kauna)
Baban ango sannu (ango da amarya na kukan 'kauna)
Kaima na gaisheka (ango da amarya na kukan 'kauna)
Baba na amaryar mu (ango da amarya na kukan 'kauna)
Kaima na gaisheka (ango da amarya na kukan 'kauna)
Dangin ango sunzo (ango da amarya na kukan 'kauna)
Kuma na gaisheku (ango da amarya na kukan 'kauna)
'kawaye na amarya (ango da amarya na kukan 'kauna)
Kuma na gaisheku (ango da amarya na kukan 'kauna)
Abokan angon nan (ango da amarya na kukan 'kauna)
Kuma na gaisheku (ango da amarya na kukan 'kauna)
Ina auntys ango (ango da amarya na kukan 'kauna)
Kuma na gaisheku (ango da amarya na kukan 'kauna)
Auntys na amaryar nan (ango da amarya na kukan 'kauna)
Kuma na gaisheku (ango da amarya na kukan 'kauna)
Zama na amana zakuyi aure shi akewa alfarma
Me ya faru da juna ne? Naga amarya na kokawa
Kukan dadi ne angonta yanata shash-sharewa
Me ya faru da juna ne? Naga amarya na kokawa
Kukan dadi ne angonki yanata shash-sharewa
Me ya faru da juna ne? Naga amarya na kokawa
Kukan dadi ne angonta yanata shash-sharewa
Written by: RR
instagramSharePathic_arrow_out